Sojojin sun kashe ‘yan Boko Haram 11 da kwato makamai a Adamawa
Rundunar sojojin Najeriya ta ce, dakarunta sun yi nasarar kashe mayakan Boko Haram 11 a wani sabon da hari da ‘yan kungiyar suka shirya kaiwa a garin Madagali da ke karamar hukumar Madagali jihar Adamawa. Mataimakin Daraktan hulda da jama’a Kanal Ado Isa, ne sanar da hakan ya kuma ce, sojojin Operation Lafiya Dole ne […]
Rundunar sojojin Najeriya ta ce, dakarunta sun yi nasarar kashe mayakan Boko Haram 11 a wani sabon da hari da ‘yan kungiyar suka shirya kaiwa a garin Madagali da ke karamar hukumar Madagali jihar Adamawa.
Mataimakin Daraktan hulda da jama’a Kanal Ado Isa, ne sanar da hakan ya kuma ce, sojojin Operation Lafiya Dole ne suka yi nasarar kashe ‘yan kungiyar tare da kwato muggan makamai daga hannun maharan a jiya Laraba.