Sokari ya sanya wa kulob din Esperence hannu
dan kwallon Najeriya na ’yan kasa da shekara 20 (U-20) wanda ya halarci gasar cin kofin duniya na ’yan kasa da shekara 20 da ya gudana a Newzealand Kingsley Sokari ya bar kulob din Enyimba, inda ya sanya wa kulob din Esperence na Tunisiya hannu. dan kwallon ya samu nasarar sanya wa kulob din hannu […]
dan kwallon Najeriya na ’yan kasa da shekara 20 (U-20) wanda ya halarci gasar cin kofin duniya na ’yan kasa da shekara 20 da ya gudana a Newzealand Kingsley Sokari ya bar kulob din Enyimba, inda ya sanya wa kulob din Esperence na Tunisiya hannu.
dan kwallon ya samu nasarar sanya wa kulob din hannu ne na tsawon shekara uku bayan yarjejeniyar da suka kulla a tsakaninsa da kulob din da kuma amincewar da aka samu a tsakanin kulob dinsa na Enyimba da ke Aba da kuma na Esperence da ke Tunisiya.
dan kimanin shekara 20, a ranar Litinin da ta wuce ne ya sanya hannun a kwantaragin da ba a fadi kudin ba.
Sai dai ba zai buga wa kulob din Esperence gasar cin kofin kalubale na Afirka (CAF Confedaration Cup) ba, ganin ya riga ya yi wa kulob din Enyimba wasa a gasar zakarun kulob-kulob na Afirka (Champions League) a bana.
Kulob din Esperence dai ya dade yana sayen ’yan kwallon Najeriya. Garba Lawal yana daga cikin ’yan kwallon da suka taba yi wa kulob din wasa kafin ya koma Turai inda ya yi wasa a kulob da dama.