Soke aikin hajji: An daina yi wa maniyyata bita a Yobe
An daina yi wa maniyyatan bita bayan soke aikin hajjin ‘yan ketare da Saudiyya ta yi.
An dakatar da yi wa maniyyatan Jihar Yobe bita biyo bayan hukuncin da Kasar Saudiyya ta zartar na takaici Aikin Hajjin bana ga mazauna kasarta kadai.
Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da Shugaban hukumar, Alhaji Bukar Kime (Aji Sudanin Damaturu) ya aike wa da Aminiya.
- Majalisa na son sabon Hafsan Sojin Kasa ya magance matsalar tsaro
- Iyayen daliban Islamiyyar Tegina sun fara barar kudin fansar ’ya’yansu
Yayin wani taro da aka gudanar, Bukar Kime ya fadakar da maniyyatan halin da ake ciki na soke zuwa aikin hajjin na wannan shekara ta 2021 wanda Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Kasa (NAHCO) ta aiko musu a shelkwatar hukumar da ke Damaturu, babban birnin Yobe.
Bukar Kime ya kirayi maniyatan da cewa su jira ko za a samu wani canji daga Hukumar ta NAHCO, inda duk wani canji da aka samu za a kira su a shaida musu.
Sannan sai ya hore su da cewa shi ya sa Allah ya yi su musulmi saboda haka su rungumi wannan canji a matsayin kaddara.
Kazalika, ya tabbatar musu da cewa kudaden su suna nan a ajiye a wajen Hukumar Jin Dadin Alhazan ta Yobe, kuma duk wani shirye-shirye sun kammala na ganin an mayar wa duk wani maniyyaci kudinsa, wanda kuma yake so a ci gaba da ajiye masa za su ajiye zuwa badi.
A makonnin da suka gabata ne Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Yobe ta fara gudanar da yi wa maniyata aikin hajjin bana na shekara ta 2021 bita kan aikin hajjin.
Saudiyya dai ta takaice Hajjin na bana ga mazauna kasarta kadai kan abin da ta kira fafutikar ci gaba da yaki da dakile yaduwar annobar cutar Coronavirus.