Soke zaben Abba: ’Yan kasuwa na rufe shaguna saboda fargabar rikici

Soke nasarar Abba Kabir Yusuf da kotu ta yi a matsayin Gwamnan Jihar Kano ke da wuya, ’yan kasuwa suka fara rufe shaguna suna tafiya gida

Soke zaben Abba: ’Yan kasuwa na rufe shaguna saboda fargabar rikici

Soke nasarar Abba Kabir Yusuf da kotu ta yi a matsayin Gwamnan Jihar Kano ke da wuya, ’yan kasuwa suka fara rufe shaguna suna tafiya gida.

Aminiya ta lura cewa galibin ’yan kasuwa a kasuwannin Sabon Gari, Kantin Kwari da Singa, na ta rige-rigen rufe shaguna suna tafiya gida.

Kazalika, kawo yanzu babu wani shagali ko murna daga magoya bayan APC da yake gudana.

Hatta magoya bayan APC da Aminiya ta lura sun taru a wasu muhimman tituna da ke kusa da kotun yanzu duk sun watse, sun kama gabansu.

Bin diddigi: Gaskiyar batun kai hari a Bankin CBN

NAJERIYA A YAU: Lakurawa muka kai wa hari a Sakkwato —Sojoji

Manyan alhinin Najeriya a 2024

’Yan sanda sun kama waɗanda suka shirya rikicin ‘yan daba a Kano