Solomon Dalong da Dambazau da tsofaffin gwamnoni za su zama ministocin Buhari
Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Abubakar Bukola Saraki ya tabbatar da karbar jerin sunayen ministocin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai nada a gwamnatinsa. Sanata Saraki ya fadi a cikin shafinsa na Tweeter cewa ya karbi sunayen ne da misalin karfe 5:00 na yammacin shekaranjiya Laraba inda cewa: “Ina tabbatar muku cewa yanzun nan na karbi […]

Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Abubakar Bukola Saraki ya tabbatar da karbar jerin sunayen ministocin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai nada a gwamnatinsa.
Sanata Saraki ya fadi a cikin shafinsa na Tweeter cewa ya karbi sunayen ne da misalin karfe 5:00 na yammacin shekaranjiya Laraba inda cewa: “Ina tabbatar muku cewa yanzun nan na karbi sunayen.”
Shugaban Ma’akatan Shugaban kasa Alhaji Abba Kyari da Babban Mai taimaka wa Shugaban kasa kan Al’amuran Majalisar Dattawa Sanata Ita Enang suka kai sunayen ga Sanata Saraki a wata ambulan da ke like..
Sai dai Sanata Saraki ya ce ba za su fadi ko su wane ne Buhari ya zaba don nada su ministoci ba sai ranar Talata mai zuwa a cikin zauren majalisa.
Kakakin Sanata Saraki, Yusuph Olaniyonu ya ce: “Bisa ga al’adar Majalisar Dattawa ta yanke shawarar ambular din ta kasace a like sai ranar Talata 6 ga Oktoba lokacin zaman majalisar inda za a bude domin karanta wa sanatoci.”
Ya ce dalilin haka kuwa shi ne saboda jiya Alhamis ana hutun ranar samun ’yancin kai, kuma majalisa ba ta zama a ranakun Juma’a da Asabar da Lahadi da Litinin.
Fadar Shugaban kasa kuma ta ce ba huruminta ba ne ta gaya wa jama’a ko su wane ne ta zaba sai majalisa ta gani.
Sai dai wasu kafafen labarai sun ce ruwaito cewa wadansu majiyoyin kusa da Jam’iyyar APC sun shaida musu cewa tsofaffin gwamnoni da tsofaffin sanatoci da kwararru suna cikin sunayen da aka mika wa majalisar.
Daga cikin wadanda aka ce akwai sunayensu a cikin wadanda aka mika sunayensu akwai fitaccen dan rajin kare hakkin jama’ar nan Barista Solomon Dalong da tsohon Hafsan Hafsoshin Sojin kasa Janar Abdurrahman Dambazau da tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP ta kasa kuma jigo a Jam’iyyar APC Mista Audu Ogbeh da jagoran APC na shiyyar Kudu maso Gabas kuma tsohon Shugaban Jam’iyyar ANPP, Dokta Ogbunnaya Onuh.
Tsofaffin gwamnonin da aka mika sunayensu ga Majalisar Dattawan don tace su, sun hada da Darakta Janar na Yakin Neman Zaben Shugaba Buhari kuma tsohon Gwamnan Jihar Ribas Rotimi Chibuike Amaechi da tsohon Gwamnan Jihar Legas Babatunde Fashola da takwaransa na Ekiti Kayode Fayemi da tsohon Gwamnan Jihar Anambra Sanata Chris Ngige da tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Neja Alhaji Ahmed Musa Ibeto da ’yar takarar Gwamnan Jihar Taraba a karkashin Jam’iyyar APC Hajiya Jummai Alhassan.
Sauran su ne Babban Lauya Abubakar Malami (SAN) da Hajiya Amina J. Mohammed tsohuwar mashawarciyar Shugaban kasa kan shirin Muradun karni da tsohuwar Kwamishinarb Kudi ta Jihar Ogun Misis Kemi Adeosun wadda aka ce an mika sunanta ga majalisar jiharta don sake nada ta Kwamsihina.
Akwai kuma Sanata Hadi Sirika wani matukin jirgin sama da ya wakilci Katsina ta Arewa a Majalisar Dattawa daga shekarar 2011-2015 a karkashin Jam’iyyar CPC, sai Babban Manajan daraktan Kamfanin Mai na kasa (NNPC) Ibe Kachikwu da ake jin za a nada Minista a Ma’aikatar Man fetur bayan da Shugaba Buhari ya bayyana cewa shi zai rike Ministan Man fetur da kansa.
Sauran su ne Udoma Udo-Udoma da Suleiman Adamu da Osagie Ehanire da kuma Ibrahim Jibril.
Jama’a sun rika dako ganin sunayen ministocin tun bayan da Shugaba Buhari ya ce zai mika sunayensu ga majalisar kafin karshen watan Satumban da ya gabata, sai dai har zuwa tashi daga zaman majalisar a shekaranjiya Laraba ba ta samu jerin sunayen ba har Shugaban Majalisar, Sanata Abubakar Bukola Saraki ya sanar da dage zamanta zuwa Talata da sanatoci za su koma bakin aiki.