Solskjaer ya zama sabon kocin Besiktas

Solskjaer ya zama kocin Besiktas bayan shafe fiye da shekaru yana zaune babu aiki.

Solskjaer ya zama sabon kocin Besiktas

Tsohon kocin Manchester United, Ole Gunner Solskjaer, ya zama sabon mai horas da ƙungiyar Besiktas da ke Turkiyya.

Solskjaer ya zama kocin Besiktas bayan shafe fiye da shekaru yana zaune babu aiki.

Kocin ɗan ƙasar Norway wanda United ta sallama a watan Nuwamban 2021, zai maye gurbin Giovanni van Bronckhorst wanda a Nuwamban bara Besiktas ɗin ta raba gari da shi.

Cikin sanarwar da ƙungiyar da ke Istanbul ta fitar a ranar Asabar, ta ce ƙulla yarjejeniyar da Solskjaer zuwa ƙarshe kakar wasanni ta bana da zaɓin ƙarin kaka ɗaya.

Solskjaer ya buga wa United fiye da wasanni 200 a lokacin da yake ɗan wasan gaba kuma ɗaya daga cikin waɗanda suka kasance a ƙungiyar a lokacin da ta zama gagarabadau a kakar wasa ta 1998-99.

Bayan ya ajiye buga tamaula ne Solskjaer ya shiga aikin horaswa inda ya shafe shekaru da dama a ƙungiyar Molde da ke Norway gabanin tafiya United a 2018.

A halin yanzu dai Besiktas ce ta shida a teburin gasar Super Lig ta Turkiyya, inda akwai tazarar maki 21 tsakaninta da Galatasaray da ke saman teburin.

Haka kuma, akwai tazarar maki 12 tsakaninta da ƙungiyar Fenerbahce wadda Jose Mourinho ke jagoranta.

DSS ta kama ’yan Boko Haram 10 a Osun

Mutum 60 sun mutu a fashewar tankar mai a Neja

Solskjaer ya zama sabon kocin Besiktas

Nijeriya ta zama abokiyar hulɗar ƙungiyar BRICS