‘Son banza’
Barkanmu da warhaka Manyan gobe. Da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku wani labari ne mai taken: ‘Son Banza’. Labarin na kunshe ne da yadda yakamata Manyan gobe su zama masu godiya ga iyaye don samun albarka. Taku: Amina Abdullahi Akwai wani dan kasuwa Malam Ali. Yana da mata da ‘ya’ya […]
Barkanmu da warhaka Manyan gobe. Da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku wani labari ne mai taken: ‘Son Banza’. Labarin na kunshe ne da yadda yakamata Manyan gobe su zama masu godiya ga iyaye don samun albarka. Taku: Amina Abdullahi
Akwai wani dan kasuwa Malam Ali. Yana da mata da ‘ya’ya biyu. Suna da rufin asiri daidai gwargwado. Sannan kuma Allah Ya ba su wata kyakkyawar kaza wadda take yin kwai a kullum.
Wani abin mamaki da burgewa da kuma daukar hankali shi ne kazar kwan gwal take yi. Don hadama Ali sai ya rika ganin kazar na bata masa lokaci kuma yana so ya samu duk kwayayen da take masa a lokaci guda.
Rannan sai ya yanke shawarar yanka kazar don ya kwashe duka kwayayen da ke jikinta.
Washe gari, kazar ta yi kwai kamar yadda ta saba. Domin son banza da hadama da kuma gaggawa, sai ya samu wuka mai kaifi, ya kamo kaza ya yanka sannan ya huda cikinta ko zai kwaso kwayaye. Bude cikin kazar ke da wuya sai bai ga komai a ciki ba in ban da jini da sauran kayan ciki kuma babu kwai ko daya a ciki. Sai aka wayi gari, kwayayen da yake samu kullum yana sayarwa ya rasa.
Sakamakon son banza da hadama da rashin tawakkali ya fada wani hali na talauci. Kullum talaucin sai karuwa take yi har ya tsiyace.
To kun ga in mutum ya kasance mai hadama da kuma son banza ne zai wayi gari kadan dinma da yake samu ya rasa.
Ina fatan Manyan gobe za su yi amfani da wannan labarin don su zama masu godiya musamman ma ga iyaye. Saboda duk wanda yake da dogon buri idan bai yi hattara ba zai fada ga halaka.