Son cin bulus ne ya jefa mu cikin matsalar tattalin arziki – Dogara
Shugaban Majalisar Wakilai Honorabul Yakubu Dogara ya ce halin matsin tattalin arzikin da kasar nan ciki ya faru ne sakamakon dabi’ar nan ta son a ci bulus.Honorabul Yakubu Dogara, ya bayyana haka ne a lokacin addu’ar nuna godiya ga ’ya’yan Honorabul Olusegun Odebunmi a cocin The Citizens Church da ke Abuja, inda ya ce ’yan […]
Shugaban Majalisar Wakilai Honorabul Yakubu Dogara ya ce halin matsin tattalin arzikin da kasar nan ciki ya faru ne sakamakon dabi’ar nan ta son a ci bulus.
Honorabul Yakubu Dogara, ya bayyana haka ne a lokacin addu’ar nuna godiya ga ’ya’yan Honorabul Olusegun Odebunmi a cocin The Citizens Church da ke Abuja, inda ya ce ’yan Najeriya musamman Kiristoci suna da hujjar da za su yi murnar Ranar Dimokuradiyya, kamar yadda Kakakinsa Turaki Hassan ya fadi a wata sanarwa. “Dukkan kalubalen da muke fuskanta sakamakon zabinmu ne, a lokacin da muka fuskanci yanayi na zabi mai wahala, sai mu zabi bulus, kuma wannan ne ya sa muka samu kanmu a tsaka-mai-wuya,” inji shugaban majalisar.
Shugaban wanda ya nuna damuwa kan wahalhalun da suke fuskantar iyalai da al’umma sakamakon karuwar farashin kayayyakin bukatun yau da kullum, ya ce an kwadaitar da mabiya addinin Kirista su rika godiya ga Allah a duk halin da suka samu kansu, musamman kan yadda dimokuradiyya ta bayar da ’yancin bauta.
Ya ce lokaci ya yi da al’umma za ta koma ga Ubangiji domin neman mafita maimakon surutai da koke-koke, inda ya ce: “Ta hanyar addu’o’i Ubangiji zai iya daukaka marasa galihu daga cikin al’umma su bayar da tasu gudunmawar wajen bunkasa kasa tare da sake fasalinta. ’Yancin da muka samu wato dimokuradiyya da muka sadaukar da kai a kanta, ba tana nufin mutum ya yi duk abin da ya ga dama ba ne. A’a alkawari ne na cewa al’umma mai ’yanci kamar tamu za su iya samun kasar da ta dace da bukatarsu.”
Dogara ya ce “Farashin man fetur ya fadi daga Dala 110 kan kowace ganga zuwa Dala 40, kuma saboda rikicin yankin Neja-Delta, a da muna samun Dala 110 kan ganga miliyan 2 da dubu 200 a kowace rana, amma yanzu Dala 40 sau miliyan 1 da dubu 200 a rana. Don haka kun ga dukiyar kasar nan ta yi kasa sosai kasa da kashi 50 cikin 100.”
Ya kara da cewa: “Abin takaici, shi ne a lokacin da muke cikin yalwa ba mu zuba jari mun fadada hanyoyin karuwar arzikinmu ba, don haka muka iske kanmu a tsaka-mai-wuya. Hanyar ba za ta zamo mai sauki ba, amma gaskiyar ita ce galibin hanyoyin da ake bi a kai ga nasara ba masu dadin bi ba ne.”
Sai ya taya Honorabul Odebunmi kan haihuwar tagwaye da ya samu, inda ya bukaci iyaye su tarbiyyantar da ’ya’yansu a kan hanyar Ubangiji.