Son gyara tarbiyya ya sa aka kawo mini hari – Jidda Usman

Malam Abubakar Jidda Usman shugaban Sashen Labarai da Al’amuran Yau da kullum na gidan Radiyon Freedom dake Kaduna, ya bayyana wasu dalilai da yake ganin suka sa wasu yan ta’adda suka kai masa hari a gidansa dake Kwaru Badarawa. A cewarsa, yana ganin an kai masa hari ne saboda ra’ayinsa akan ganin an gyara tarbiyar […]

Son gyara tarbiyya ya sa aka kawo mini hari – Jidda Usman

Malam Abubakar Jidda Usman shugaban Sashen Labarai da Al’amuran Yau da kullum na gidan Radiyon Freedom dake Kaduna, ya bayyana wasu dalilai da yake ganin suka sa wasu yan ta’adda suka kai masa hari a gidansa dake Kwaru Badarawa.

A cewarsa, yana ganin an kai masa hari ne saboda ra’ayinsa akan ganin an gyara tarbiyar matasa a unguwarsa da ma jihar nan.

Ya ce a matsayinsa na limami a masallacin Kwaru da ke a Unguwar Badarawa yana yawan magana akan yadda tarbiyar yara, musamman matasa ke tabarbarewa ba tare da iyaye suna daukar matakin magance hakan ba.

Malam Jidda ya bayyana hakan ne a zantawarsa da manema labarai a gadon asibitin Garkuwa, inda yake kwance yana karbar magani a sakamakon rauni da ya samo a wuya da hannunsa.

Shi dai Jidda, wanda dan jarida ne wasu da ba’a san ko su wane ne ba suka kai masa hari a gidansa a daren wataLitinin da misalin karfe biyun dare.

Ya ce bai ga dalilin da iyaye zasu rika boye ’ya’yansu dake aikata laifuffuka a Unguwar ba.

‘ Idan yaro ya shiga kungiyar yan Sara-suka kuma yana ajiye makamansa a cikin gidan iyayensa,sannan iyayen suna kawar da kai bai da ce ba, har ma su nemi a saki yaron idan an kama shi.

‘Amma idan aka kama shi sai kaga su iyayen ne kan gaba wajen zuwa neman a sake shi, komai girman laifin da ya aikata,”inji shi.

A cewarsa, yana zaune a Unguwar Badarawa tun shekarar 1975 har ya zuwa lokacin da ya tashi ya koma gidansa a Kwaru shekaru 15 da suka wuce.

Ya kuma bayyana yadda ta kwashe tsakaninsa da daya daga cikin maharan.

“ Da misalin karfe biyu na dare na fito bandaki a kan hanya ta komawa daki sai na ga mutum makale a bango rike da wuka. Daga nan muka fara kokowa har ya yanke ni sannan ya gudu, “inji shi.

Ya ce shi mutum ne dake zaman lafiya da kowa dukkuwa da cewa yana yawan magana akan tarbiyar mutane, musamman idan yaga an aikata ba daidai ba.