SON ta karrama kamfanoni 30 kan samar da kayayyaki masu inganci a Kano

Hukumar ta buƙaci kamfanonin su zama jakadu nagari wajen samar da kayayyaki masu inganci.

SON ta karrama kamfanoni 30 kan samar da kayayyaki masu inganci a Kano

Hukumar Kula da Ingancin Kayayyaki ta Najeriya (SON), ta karrama kamfanoni 30 a Jihar Kano, da takardun shaidar cika ka’idojin wajen samar da kayayyaki masu inganci.

Jami’in SON a Kano, Ado Ibrahim ne, ya gabatar da takardun shaidar a madadin Babban Daraktan hukumar, Dokta Efeanyi Okeke.

Dokta Okeke, ya taya kamfanonin murna bisa samun shaidar amincewa da kayayyakinsu, inda ya bayyana cewa hakan ya nuna cewa suna samar da ingantattun kayayyaki a kasuwannin Najeriya.

Ya yaba wa kamfanonin bisa cika ka’idojin da ake bukata don samun shaidar SON.

“An gwada kayayyakinku kuma an tabbatar da sun cika ƙa’idojin da ake buƙata,”in ji shi.

Sai dai ya buƙaci kamfanonin da su ci gaba da aiki tare da SON don samar da kayayyakin da ake buƙata a kasuwanni.

“Ku zama wakilanmu a waje. Idan kuna sayar da kayayyakinku, ku tabbatar wa kwastomominku cewa kayanku daga SON suke.”

Kazalika, ya bayyana cewa takardun shaidar za su shafe tsawon shekara guda ne, kafin daga bayan kamfanonin su sake sabunta su.

Ya jaddada fa’idar samun shaidar SON, kamar damar kare sunan kamfani daga masu samar da jabun kayayyaki.

“Idan wani ya samar da irin kayayyakinku, ba zai samu tambarin SON ko lambar rajista ba. Kuna iya kai rahotonsa wajenmu, kuma za mu taimake ku mu kare kamfaninku,” in ji Dokta Okeke.

Haka kuma ya bayyana cewa SON ta ƙudiri aniyar samar da bayanan kamfanonin da suka samu takardar shaida domin kare sunayensu domin kaucewa masu buga jabun kayayyaki.

“Mu a SON, muna da shirin samar da bayanan kamfanonin da suke sayar da kayayyaki domin a iya bibiyar kayayyakin idan wata matsala ta taso,” ya bayyana.

Ya ce za ake buga tambarin SON da lambar rajistar kamfanonin a kan kayan da suke fitarwa domin tabbatar da ingancin kayan ga kwastomomi.

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu

Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025

Tinubu ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa

HOTUNA: Ana shirye-shiryen jana’izar marigayi Lagbaja