Son uwar giji

Sannu-sannu dai makircin Turawan Yammacin Turai da Amurka don zaluntar kasar nan sai kara bayyana yake yi, kuma a game da haka ana iya cewa kifi ya kasa  ganin mai jan koma, domin matsalolin da suka hana Najeriya lami-lafiya duk sun samo asali ne daga kutungwilar Yahudu da Nasara don tatse arzikinta. Wadannan Turawan sun […]

Son uwar giji
Son uwar giji

Sannu-sannu dai makircin Turawan Yammacin Turai da Amurka don zaluntar kasar nan sai kara bayyana yake yi, kuma a game da haka ana iya cewa kifi ya kasa  ganin mai jan koma, domin matsalolin da suka hana Najeriya lami-lafiya duk sun samo asali ne daga kutungwilar Yahudu da Nasara don tatse arzikinta. Wadannan Turawan sun dade suna kulafucin moriyar dimbin arzikin man fetur da na ma’adinai da na kasar noma mai albarka fiye da al’ummomin cikinta. Sun fahimci cewa haka nan kawai, zikau-mikau ba za su yi galba ba, muddin dai ba sun haddasa masifun da za su rarraba kawunan jama’a ne ba, ta yadda hakan zai ba su damar shiga tsakaninsu don haddasa bakar gabar da za ta tayar da zaune tsaye, har ta kai sai an neme su don kawo maslaha, ko su kukkutsa  kasar da karfin tsiya, wai don kare mutuncin ‘yan kasashensu da kuma harkokin kasuwancinsu.
A cikin ‘yan shekarun da suka gabata wadannan kasashen sun yi nasarar haddasa fitintinu iri-iri da suka wanzar da rikice-rikicen addini da kabilanci, wadanda a yanzu sun yi tasiri kwarai wajen rarraba kawunan jama’an Kudanci da na Arewacin kasar nan, sun kuma yi nasara wajen cusa ra’ayin addini a zukatan ‘yan Najeriya, wajen aiwatar da dukkan manufofin gwamnati ko wanzar da harkokin zamantakewa.  A yanzu kuma wadannan al’amura sun yi kamari, suna neman kai kasar kasa kamar yadda mayaudaranta suka tsara.
Take-taken wadannan kasashe da kamfanoninsu don samun galba ga kasashe masu tasowa da ke da  albarkatu masu yawa, kan dauki dogon lokaci kafin su biya musu bukata, domin kuwa tamkar cutar sankara suke, a hankali-a-hankali suke gawurta. Amurka tare da kawayenta na nahiyar Turai sun dade suna kwallafa ransu kan arzikin man fetur da ke yankin Guinea Gulf a tekun Atlantika, wanda ya hada da kasashen Najeriya da Kamaru da Gabon da Angola. Dabararsu ta cin gajiyar wannan albarkar ita ce ta kafa wata rundunar da suke kira Guinua Gulf High Command, wacce za ta ba su sukunin jibge rundunoninsu a yankin da zimmar bayar da kariya ga kasashen daga hari daga wasu kasashe ko kuma don maganin masu tayar da kayar baya a cikin kasashen.
Ko da yake gwamnatocin wadannan kasashe na Guinea Gulf sun sha kai ruwa rana a dukkan lokutan da wadancan kasashen Turai da Amurka suka nemi iznin jibge askarawansu a wannan wurin, amma sai ga shi a yanzu kasashen Amurka da Faransa da Birtaniya da Jamus sun bayar da sanarwar samar da jiragen ruwan yaki da dakarun da za su jibge a yankin Guinea Gulf, wai don su taimaki Najeriya yaki da barayin danyen mai wadanda ke gurgunta tattalin arzikin kasar.  Tun ba yau ne ba ake ta satar danyen man kasar nan ba kakkautawa, kuma a kasashen wadannan Turawan ne ake dillancin sa, tare da sanin gwamnatocinsu. Ko a bara waccan sai da Shugaba Goodluck Jonathan ya nemi taimakonsu don a kawo karshen wannan musifar, amma sai suka ce da shi idan yana son haka sai ya hana satar man da suka ce manyan jami’an gwamnatinsa ne ke ficewa da shi, suna karyarwa a kasashensu. Amma, a cewarsu,  tun da ya san barayin danyen man, ya kuma kasa hana su, to su ina ruwansu.
Ana iya cewa wadannan Turawan ne ke daure wa barayin mai gindi,  don daga bisani su samu hujjar kutsowa kasar, kamar yadda aka tabbatar da cewa su ne ke tarairayar ‘yan ta’addar da ke tayar da yamutsi a Arewacin kasar nan da sunan addini.  Haka nan kuma babu ta yadda za a yi nasara game wannan ba tare da sanin jami’an Gwamnatin Najeriya ba, domin kuwa idan don saboda satar mai ne za a amince a jibge dakarun kasashen ketare a gabar ruwan kasar nan, me ya hana rundunonin ruwan Najeriya magance wannan matsalar? Da gangar ne aka raunana rundunonin ruwan Najeriya don a fake da haka a bayar da iznin jibge dakarun kasashen ketare da wata manufa can daban.  To wane tabbaci za a bayar cewa kasancewar rundunonin kasashen ketare a bakin tekun kasar nan zai iya magance matsalar satar man?
Baicin haka nan kuma ana cewa arzikin man fetur din da ke jibge ne a sashen Arewa-maso-Gabas na Najeriya ya haddasa tashe-tashen hankula da kasashen Turai ke assasawa, ta yadda za su ji dadin mallakar makaman filayen da ke da dimbin arzikin man fetur da iskar gas a yankin Tafkin Chadi, ta yadda nan gaba za su rika fitar da man da kuma iskar gas din ta wasu bututun da za su shimfida tun daga yankin, har ya zuwa yankin Bakassi mai arzikin man fetur wanda ke makwabtaka da  sauran kasashen da ke da dimbin arzikin man fetur, daga nan ne kuma za a ji dadin kwashewa a jiragen ruwa zuwa kasashensu.
Muddin wadanan dakarun suka samu samu gindin zama a gabar Guinea Galf, za su kara rura wutar hayaniyar da sassan kasar nan ke yi kan mallakan man fetur, kuma da zaran hakan ya yi kamari sai a nemi mamaye yankin Neja-Dalta, mai arzikin man fetur da zimmar hana sauran al’ummomin kasar nan amfana da shi. Wannan shi ake kira son uwar giji.