Son zuciya ke sanya batagari shigowa da miyagun kwayoyi – Dalha Wadace
Bayanai sun ce duk da matakin da Gwamnatin Tarayya ta dauka na rufe iyakokin kasa ana samun batagari da ke shigowa da kayayyakin da aka haramta ciki har da miyagun kwayoyi. A zantawar da Aminiya ta yi da Babban Jami’in Hukumar Kwastam da ke kula da Iyakar Seme a Legas, Dalha Wadace ya bayyana yadda […]
Wani sashi na man fetur da Hukumar Kwastam ta kama a iyakar Najeriya da kasar Benin a yankin Seme
Bayanai sun ce duk da matakin da Gwamnatin Tarayya ta dauka na rufe iyakokin kasa ana samun batagari da ke shigowa da kayayyakin da aka haramta ciki har da miyagun kwayoyi. A zantawar da Aminiya ta yi da Babban Jami’in Hukumar Kwastam da ke kula da Iyakar Seme a Legas, Dalha Wadace ya bayyana yadda batagarin ke fasakwaurin da matakan da hukumar ke dauka domin dakile su.
Aminiya: Jama’a suna mamakin yadda ake ci gaba da fasakwaurin kayan da aka haramta shigowa da su duk da rufe iyakoki yaya abin yake?
Dalha Wadace: Ka san rufe iyakar da aka yi hani ne da aka yi kan shigowa ko fita da kayayyaki ta kan iyakokin kasa amma ba a hana fice da shigar jama’a a kan iyakokin kasa ba. Domin idan mutum yana da cikakkun takardunsa na shige- da-fice yana da damar shiga ko fita ta kan iyakokin, a irin haka ne ake samun wadansu batagari da ba sa kishin kasa suke amfani da damar suna shigo da haramtattun kayayyakin kamar miyagun kwayoyi.
Amma jami’anmu a kowane lokaci idonsu a bude yake wannan ne ya sa ka ga a lokuta da dama muna kama miyagun kwayoyin duk da dabarar da ake yi domin yin bad-da-kama. Wannan ne ya sa a kwanakin baya muka kama tarin miyagun kwayoyi da aka yi fasakwaurinsu a motar fasinja ta wani babban kamfani.
In ka lura ba da masaniyar kamfanin ba ne kuma ba duka matafiya ke da alhakin fasakwaurin kwayoyin ba, a’a wadansu batagari ne suka yi aikin, don haka a kowane lokaci muna shirye, da zarar sun shigo za mu ci gaba da kama su.
Aminiya: Ana alakanta tabarbarewar tarbiyyar matasa da miyagun kwayoyin, ka amince da haka?
Dalha Wadace: Tabbas matsaloli da dama da ake fama da su na rashin tsaro da gurbatar tarbiyya na da alaka da miyagun kwayoyin. Wannan ne ya sanya Gwamnatin Tarayya daukar kwararan matakai a kan haka. Kana mu da aka dora wa alhakin kula da kan iyakar kasarmu muna yin aiki tukuru domin dakile muguwar dabi’ar, kuma muna samun nasarori sossai a kan aikin.
Aminiya: Akwai dokar hana sayar da man fetur a nisan kilomita 20 daga kan iyakar kasa, ko kuna kama irin wannan man fetur na fasakwauri?
Dalha Wadace: Haka abin yake, masu fasakwaurin man fetur a jarkoki suna yin dabaru irin nasu. Mu kuma kowane lokaci muna sane da su muna dakile yunkurinsu wannan ne ma ya sanya a kowane lokaci muke kama man fetur na fasakwaurin. Muna kama su a kullum kuma ba za mu gajiya ba. Shawarata ga masu fasakwauri ita ce su nemi sana’a, domin fasakwauri ba aikin kwarai ba ne. Idan suka nemi halatacciyar sana’a sun huta wa kansu, domin gwamnati ba za ta zuba ido wadansu su yi wa tattalin arzikin zagon kasa ba.