Son zuciya ne ya haifar da koma-bayan dimokuraɗiyya a Nijeriya – Sani GNPP

Ɗan siyasar ya koka da irin salon siyasar da ake yi a yanzu.

Son zuciya ne ya haifar da koma-bayan dimokuraɗiyya a Nijeriya – Sani GNPP

Wani ɗan Arewa mazaunin garin Ile­Ife a Jihar Osun, Alhaji Sani GNPP wanda ya yi fice a harkar siyasar ‘yan Arewa a Kudu maso Yamma, ya yi tir da mummunar siyasar da ake yi yanzu a tsakanin wasu shugabanni da ƙusoshin jam’iyun siyasa a Nijeriya.

Ya ce “irin wannan gabar siyasa a tsakanin shugabanni ta taimaka wajen sukurkucewar dimuƙraɗiya da rabuwar kawunan magoya da taɓarɓarewar tsaro tare da durƙusar da tattalin arziƙin ƙasa.”

Ya faɗi haka ne cikin hirar da ya yi da Aminiya, inda ya kawo misali da jihohin Zamfara da Kano da Ribas da Kaduna.

A cewarsa, “tsofaffin gwamnoni da waɗanda ke kan mulki da ƙusoshin jam’iyu sun fito da son zuciyarsu a fili domin dagula al’amura da gangan da suka haifar da koma-bayan dimukraɗiya”.

Ya ce, “muddin irin waɗannan shugabanni za su ci gaba da gudanar da mummunar gabar siyasa, to kamata ya yi su tattara nasu-ya-nasu su fice kwata-kwata daga harkar siyasar Nijeriya.”

Ya gargaɗi irin waɗannan shugabanni, musamman a Arewacin ƙasa kada su kuskura su bari Arewa ta zama saniyar ware.

Kuma kada su jefa Arewa a matsayin sashen da babu dattijai masu faɗa a ji.

Sani GNPP wanda ya shiga harkokin siyasa dumu-dumu tsawon shekara 45, ya shawarci shugabannin siyasa da magoya baya su yi koyi da salon siyasar tsohon Shugaban Jam’iyar GNPP na ƙasa kuma ɗan takarar Shugaban ƙasa a zaɓen shekarar 1979, marigayi Alhaji Waziri Ibrahim wanda a duk lokacin da yake yaƙin zaɓe, yake yin kira da: ‘A yi siyasa ba da gaba ba”.

Ya ce, ya yanke shawarar shiga cikin Jam’iyar GNPP a wancan zamani da laƙaba wa kansa sunan Sani GNPP ne a dalilin sha’awarsa da irin wannan kalma da dattijo Waziri Ibrahim yake yi domin zaman lafiya.

Cutar Anthrax ta ɓarke a Zamfara

Faston da ke yi wa ’yarsa fyaɗe tsawon shekaru ya shiga hannu

Trump ya rattaba hannu kan gomman dokokin zartarwa

Ƙungiya ta buƙaci rage harajin cinikayya saboda ƙuncin rayuwa