Sowore zai jawo sawarwari

A makon jiya ne mawallafin jaridar ‘Sahara Reporters’ Mista  Omoleye Sowore ya so shirya wani gangami na kasa baki daya da nufin shirya juyin-juya-hali a kasar nan, domin gyara wa gwamnati mai ci zama saboda a fadinsa ta gaza. Sai dai al’amarin nasa bai samu nasara ba domin mutane ba su amsa kiransa ba kuma […]

Sowore zai jawo sawarwari

A makon jiya ne mawallafin jaridar ‘Sahara Reporters’ Mista  Omoleye Sowore ya so shirya wani gangami na kasa baki daya da nufin shirya juyin-juya-hali a kasar nan, domin gyara wa gwamnati mai ci zama saboda a fadinsa ta gaza.

Sai dai al’amarin nasa bai samu nasara ba domin mutane ba su amsa kiransa ba kuma a halin yanzu yana can tsare a hannun jami’an tsaro na DSS ana tuhumarsa da laifin yunkurin cin amanar kasa.

Abin manaki shi ne, shi wannan Sowore din shi ne ya tsaya takarar Shugabancin Kasar nan a karkashin Jam’iyyar Africa Action Congress (AAC) kuma a lokacin zaben gwamnoni da ya gabata Babban Daraktan yakin neman zaben Shugaba Buhari,  Rotimi Ameachi ya umarci magoya bayan Jam’iyyar APC a Jihar Ribas su zabi Jam’yyar AAC ne saboda APC tana fama da rikici a jihar wanda ya sanya ta rasa dan takara a zaben Gwamna da aka gudanar. Duk da wannan karamci da Rotimi Ameachi ya yi wa Jam’iyyar AAC sai aka wayi gari yanzu Sowore ya fito yana neman ganin bayan gwamnatin da Ameachi yake ciki ta Jam’iyyar APC.

Kamar yadda mutane da dama suka bayyana ne cewa yunkurin da Sowore ya yi na haifar da juyin-juya-halin a wannan lokaci ba zai haifar da alheri ba, domin bai bi matakan da suka kamata ba kafin ya kai ga yanke wannan shawara tasa.

Ma’abota hankali sun tunatar da Sowore cewa kasashen da suka yi bore suka canja gwamnatocinsu da karfi ba su ci moriyar tayar da kayar-bayan da suka yi ba, domin al’amura sun rincabe ne a kassashen suka koma suna fuskantar wahaloli fiye da wadanda suka fuskanta kafin su yi bore su kori gwamnati.

Duk kasashen Larabawa da irin haka ta faru babu wata fa’ida da mutanen kasar suka samu,  hasali ma dai nadama da kaskanci ne sakamakon da suka samu.

Misali kasar Libya, kafin mutanen kasar su yi wa Shugaba Gaddafi bore kasa ce da kowa ke sha’awar zuwa, domin an tanadar da komai na inganta rayuwa, kowa yana jin dadi a kasar. A wancan lokacin, wani abokin aikinmu ya kai ziyara kasar ta Libya sai ya lura da zarar an idar da Sallah mutane ba su tsayawa su yi addu’a, saboda haka sai ya tambayi wani dan kasar abin da ya sanya suke haka. Da bude wannan mutumin sai ya ce “Ku ’yan Najeriya ne kuke da bukata, mu ba mu da bukatar komai.” Wato wadata ta kai wadata har ma suna ganin ba su bukatar komai a wurin Allah saboda tsananin wauta.

Da dadi ya yi wa mutanen Libya yawa sai suka tubure suka nuna cewa sun gaji da shugabansu Gaddafi don haka dole ya sauka, wannan ne ya sanya suka tayar da kayar baya har sai da ta kai an kashe Shugaba Gaddafi, amma maimakon al’ummar kasar su kara samun sa’ida sai bala’i ya fuskance su, domin a halin yanzu kasar ta koma tamkar babu shugaba. Mutanen kasar suna fama da natsalolin rayuwa, mutanen da a baya suke samun komai a huce yanzu hatta ruwan sha sai sun yi layi suke samu. Haka za ka ga mutanen kasar sun yi dogon layi domin sayen gas din girki, wanda a baya har gida ake kai musu. Wato dai canjin da suka jawo wa kansu bai yi amfani ba, hasali ma dai masifa ya zame musu.

Haka a nan Najeriya aka yi a Jamhuriya ta Farko, lokacin da aka samu shugabanni ’yan kishin kasa wadanda suka kwato wa kasar ’yanci daga Turawan mulkin mallaka kuma suka zama shugabannin kasar, inda suka yi wa  kasar aiki tsakani da Allah, amma wadansu tsageru suka kashe su, tun daga nan al’amura suka dagule wa kasar nan, domin har yanzu ba a sake samun shugabanni kamarsu ba.

A Jamhuriya ta Biyu ma an sake kwatawa,  domin a wannan lokacin da Shugaba Shehu Shagari ya karbi mulki ana sayar da buhun shinkafa Naira 35 ne, da ya gama wa’adin mulkinsa na farko shinkafa ta tashi zuwa Naira 70, haka sauran kayan masarufi farashinsu ya dan tashi, saboda haka ’yan adawa suka yi ta bata gwamnatin har sai da soja suka kwace mulki a karshen 1983, aka wayi gari ranar 1 ga Janairun 1984 da mulkin soja. Mutane sun yi ta murna an kifar da mulkin Shagari, amma maimakon al’amura su inganta sai kara tabarbarewa suka yi, domin mutane sun fuskanci matsaloli iri-iri, harkoki sun tsaya, talauci ya kunno kai sosai, kayan masarufi suka yi karanci, sai an yi layi ake samu, shinkafar da ake cewa ta yi tsada a Naira 70 aka zo ba a samunta a wannan farashi. Haka nan al’amura suka ci gaba da tabarbarewa har yanzu rayuwa ba ta koma inda take a lokacin Shagarin ba balle a samu rayuwar da ta fi ta wancan lokacin sauki.

Saboda haka yin bore a juyar da gwamnati ba shi ne mafita ba, tunda dai dimokuradiyya ake yi kuma da kuri’a gwamnatin ta shigo, to  kamata ya yi idan ana so a canja a yi amfani da kuri’a idan lokacin zabe ya yi. Wannan shi ne wayewa kuma hanya mai dorewa da za ta kai ga mafita ba tare da an zubar da jini ba.

Domin haka wannan yunkuri da Sowore ya yi na kokarin juyin-juya-hali ba zai haifar wa kasar nan da da mai ido ba, domin an yi a can baya an samu matsala, yanzu ma idan an yi babu wanda zai amfane shi. Domin haka ya kamata Sowore ya kiyayi jawo wa kansa da sauran al’ummar kasar nan sawarwari.

 

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos