Soyayya: Yadda wata ta yaudari abokina
A garin Malumfashi Jihar Katsina, shekara biyu da ta gabata, an yi wata baiwar Allah (an sakaya sunanta); wadda ta yaudari abokina ta hanyar amincewa da cewa za su yi aure. Ta amince ne bisa sharadin cewa duka bin da take so zai yi mata, domin kuwa ta ce tsohon mijinta kafin ya mutu, yana […]
A garin Malumfashi Jihar Katsina, shekara biyu da ta gabata, an yi wata baiwar Allah (an sakaya sunanta); wadda ta yaudari abokina ta hanyar amincewa da cewa za su yi aure.
Ta amince ne bisa sharadin cewa duka bin da take so zai yi mata, domin kuwa ta ce tsohon mijinta kafin ya mutu, yana yi mata komai. Ya amince amma ya ce sai dai ita ma ba za ta ci gaba da kula kowa ba, domin ya amince tun kafin aure sutura zai yi mata, sabulun wankanta da sauransu. Ta nemi cewa ya ba ta kudin domin ta fara sana’a kafin su gama shari’a a kan dukiyar mijinta, bayan an gama su yi aure.
Abokin nawa ya sayo mata atamfofi da kayan shafe-shafen mata amma da zimmar ta amince da shi su yi aure, kamar yadda suka shirya. A karshe kuwa, kawai shi yana Kano, sai dai ya ji sanarwar an yi bikinta kuma abin takaici ma, sai gas hi ta turo masa da tes din zagi ta-uwa-ta-ba, ta kuma ce ta tafi ta yi aure. Ta gargade shi cewa daga yau ya san halin mata. Haka kuma ta ce ya dauki matakin da ya ga ya yi masa daidai.
Saboda wannan yaudara da cin amana, abokina ya daina kula kowace budurwa da niyyar ya aure ta.
Tun da mu mutane ne masu addini da kyakkyawar al’ada, lallai ya kamata mu rika yi wa juna adalci. Wato babu cuta, ba cutarwa. Idan aure zai yiwu, to saurayi ko budurwa, kada wani ya yaudari wani.
Daga Ibrahim Abdullahi, Kano 08062554795