Soyayyen dankali da nama da kabeji
Assalamu alaikum Uwargida. Yaya sanyi? Allah Ya fiddamu lafiya. A yau na kawo muku yadda ake girka soyayyen dankalin turawa da nama da kabeji domin samun abun karyawa. Akwai ababe da dama wadanda za’a iya karyawa dasu. Yana da kyau a rika sauya girki daban-daban domin kada ya ginshi mutanen gidan. Shi dai wannan girkin […]
Assalamu alaikum Uwargida. Yaya sanyi? Allah Ya fiddamu lafiya. A yau na kawo muku yadda ake girka soyayyen dankalin turawa da nama da kabeji domin samun abun karyawa. Akwai ababe da dama wadanda za’a iya karyawa dasu. Yana da kyau a rika sauya girki daban-daban domin kada ya ginshi mutanen gidan. Shi dai wannan girkin ba daurasu akan wuta gaba daya ake ba. Daban ake yinsu sannan a sanyasu a wuri daya domin su kara dadi a lokacin karyawa.
Abubuwan da ake bukata
· Dankalin turawa
· Nama
· kwai
· Tumatir
· Kabeji
· Bama
· Magi
· Garin tafarnuwa
· Man gyada
Hadi
A samu dankalin turawa sannan a fere shi ba tare da daddatsa shi ba sannan a wanke a ajiye a gefe. A tafasa dankalin da ruwa da gishiri kadan sannan a tsame. A fasa kwai kamar uku sannan a zuba magi da yankakkiyar albasa kanana sosai da garin kori da na tafarnuwa domin cire karnin kwan. A daura tukunya a zuba man gyada har sai tayi zafi sannan a dauko dankali ana tsomawa a kwai ana jefawa a mangyada. Haka za a rika yi har sai sun soyu. Sannan a kwashe a zuba a rufe a kwano mai murfi.
A tafasa nama da magi da gishiri da garin tafarnuwa da na kori sannan a yayyanka mishi albasa har sai yayi laushi sosai ruwan ya kusa tsotsewa sannan a sake yayyanka albasa da timatir a zuba da man gyada kadan ayi ta gaurayawa akan wuta har sai albasar da timatir din sun nuna. Sai a kwashe a ajiye a gefe.
A samu kabeji a yayyanka shi kanana sannan a tafasa kwai kamar uku a yayyanka da dan girma a ciki sannan a sami bama da magi kadan a zuba a gauraya.
A samu kwano a zuba soyayyen dankalin a gefe, hadin nama a wani gefen sannan hadin kabeji a wani gefen.
Za’a iya hada wannan kayan karyawan da bakin shayi ko kuma mai kauri. A ci dadi lafiya!