Sridebi za ta fara fitowa a fina-finan Amurka

Idan ana batun shahararrun ’yan fim mata a kasar Indiya, Sridebi wuri gare ta na musamman saboda yadda ta shahara sosai. Babu mamaki, wannan shaharar ce ma kila ta kawo mata wata garabasar da za ta kara daga likkafarta; domin kuwa a labarin da ke rewadi, yarjejeniya ta yi nisa tsakaninta da wani kamfanin shirya […]

Sridebi za ta fara fitowa a fina-finan Amurka

’Yar wasa SrideviIdan ana batun shahararrun ’yan fim mata a kasar Indiya, Sridebi wuri gare ta na musamman saboda yadda ta shahara sosai. Babu mamaki, wannan shaharar ce ma kila ta kawo mata wata garabasar da za ta kara daga likkafarta; domin kuwa a labarin da ke rewadi, yarjejeniya ta yi nisa tsakaninta da wani kamfanin shirya fina-finai a Amurka, domin ta fito cikin wani fim da ake son shiryawa a can.

Kamar yadda bayani ya tabbatar, wani fim ne mai suna ‘Cowboys and Indian’ ake son shiryawa a Amurka, wanda Amy Redford, diyar jarumin fina-finan Amurka Robert Redford za ta jagoranta.
“Yarjejeniyar ba ta kammala ba, amma har yanzu muna kan tattaunawa.” Inji ’yar fim Sridebi, wacce kwanan nan tauraruwarta a fim ta kara habbaka, bayan da sabon fim dinta na ‘English binglish’ ya samu nasara.
A wata sabuwa kuwa, Sridebi ta ki amincewa ta fito cikin wani sabon fim mai suna ‘Fitoor’ saboda an ba ta wani gurbi da bai yi mata ba. Fim din dai, Abishek Kapoor ne ke shirya shi.
A lokacin da aka tambaye ta game da fim din, Sridebi ta ki ta ce komai amma da aka tambayi mijinta, Boney Kapoor sai ya ce: “Ba za mu ce komai ba game da wannan fim.”