SRK ya kayatar da abokiyar sana’arsa da kyautar mota jif
A Juma’ar da ta gabata ce fitaccen jarumin fina-finan Indiya, Shah Rukh Khan (SRK) ya darje wata abokiyar sana’arsa da kyautar motar hawa kirar jif.Jarumin ya ba da kyautar motar ne ga abokiyar sana’arsa, Farah Khan wanda yake daraktan fina-finan Indiya ne. A lokacin da yake bayyana dalilin kyautar, jarumin ya ce: “Wannan kyautar na […]

A Juma’ar da ta gabata ce fitaccen jarumin fina-finan Indiya, Shah Rukh Khan (SRK) ya darje wata abokiyar sana’arsa da kyautar motar hawa kirar jif.
Jarumin ya ba da kyautar motar ne ga abokiyar sana’arsa, Farah Khan wanda yake daraktan fina-finan Indiya ne. A lokacin da yake bayyana dalilin kyautar, jarumin ya ce: “Wannan kyautar na yi ta ne don na karfafa masa gwiwa sakamakon irin yadda yake aiki ba kama hannun yaro, musammma aikin da ya gudanar na fina-finai kamar su: ‘Om Shanti Om’ da ‘Main Hoon Na’ da kuma sabon fim dina na ‘Happy New Year.’
Idan dai ba a manta ba, jarumin a kai-a kai yakan yi wa abokan sana’arsa kyaututtuka, inda ya ba jarumi Abhishek Bachchan kyautar babur din kasaita wanda aka kiyasta kudinsa a kan Dalar Amurka dubu 500. A baya-bayan nan ma, akwai lokacin da ya yi wa aminiyarsa Priyanka Chopra goma ta arziki da kayan kade-kade masu matukar tsada. Sai kuma kyautar da ya ba jarumi Sanjay Dutt ta wani babur din kasaita a watan Janairun bana.
SRK dai na gab da sakin wani sabon fim dinsa mai suna ‘Happy New Year’ wanda ya kunshi jarumai kamar su Abhishek Bachchan da Boman Irani, Sonu Sood da bibaan Shah da dai sauransu.