SSANU da NASU sun yi zanga-zanga a ABU

Ba zai yiwu a biya ASUU nasu bashin ba mu kuma a kyale mu haka.

SSANU da NASU sun yi zanga-zanga a ABU

Kungiyoyin ma’aikatan jami’a na SSANU da NASU sun gudanar da zanga-zangar lumana a harabar Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.

Zanga-zangar dai wani ɓangare ne na yajin aiki da suke gudanarwa kan albashinsu da suka ce gwamnati ta rike musu na tsawon watanni huɗu a shekarar 2022.

Aminiya ta rawaito cewa, baya ga zanga-zangar da ma’aikatan suka gudanar a ranar Talata, kofofin shiga jami’ar da dama sun kasance a rufe, sannan ayyuka sun tsaya cak.

Shugaban SSANU reshen jami’ar, Kwamared Mohammed Yunusa ya roƙi gwamnati da ta yi gaggawar biyansu albashinsu da sauran buƙatunsu domin gujewa rushewar jami’o’in baki ɗaya.

“A watan Fabrairu an biya takwarorinmu na ASUU na su bashin amma mu an yi biris da mu. Kungiyoyinmu sun yi zanga-zanga kan haka, mun kuma rubuta wasika ga gwamnati amma shiru kake ji.

“SSANU na kallon hakan a matsayin rashin adalci da yunkurin kawo rabuwar kai. Jami’a ba za ta yi aiki ba ba tare da kungiyoyin nan duka ba,” in ji shi.

Don namen mulki ’yan siyasa ke sukan Tinubu —Gwamnan Kaduna

Alakarmu da El-Rufai na nan babu matsala —Uba Sani

Yau Majalisar za ta ci gaba da aiki kan Dokar Haraji

Kotu ta tsige Ohinoyi na Ƙasar Ebira