Sterling Bank abin dogaro nagari —Shugaban Givefood.ng, Kola Masha

Sterling Bank abin dogaro ne nagari, inji shugaban Givefood.ng, Kola Masha. Kola Masha shi ne Manajan-Darakta kuma shugaban shirin Babban Gona kuma jagoran Givefood.ng. Ya kammala karatun digirinsa na farko a Jami’ar Harvard, sai digirinsa na biyu a Jami’ar Fasaha ta Jihar Massachusetts da ke Amurka a bangaren injiniya. Kwararre a fannin magance matsalolin da […]

Sterling Bank abin dogaro nagari —Shugaban Givefood.ng, Kola Masha

Sterling Bank abin dogaro ne nagari, inji shugaban Givefood.ng, Kola Masha.

Kola Masha shi ne Manajan-Darakta kuma shugaban shirin Babban Gona kuma jagoran Givefood.ng.

Ya kammala karatun digirinsa na farko a Jami’ar Harvard, sai digirinsa na biyu a Jami’ar Fasaha ta Jihar Massachusetts da ke Amurka a bangaren injiniya.

Kwararre a fannin magance matsalolin da suka shafi al’umma, Mista Kola ya sami kyauta ta musamman ta fuskar matsalar rashin tsaro.

Yana kuma da kwarewa a fannin shugabanci daga manyan kamfanonin duniya a nahiyoyi har guda hudu kamar na Generic Electric (GE) Abiomed da Notore.

Kazalika yana da tarin fasahar aiki a matsayinsa na tsohon babban mai bayar da shawara ga tsohon ministan noma na Najeriya.

Ya kuma sami shaida da dama a duniya a matsayin kwararre a kan harkar noma domin riba.

A kan hakan, ya samu yabo kan yadda ya ke taka rawa wajen habbaka harkar noma a nahiyar Afrika.

Ya samu kyaututtuka da dama, ciki har da fitacciyar kyautar nan ta Eisenhower da ta Rainer.

A cikin wannan tattunawar, ya yi bayani dalla-dalla a kan hadin gwiwar da suke yi da bankin kasuwanci na Sterling a karkashin shirin Givefood.ng, yana mai cewa bankin ya taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarar shirin.

Givefood.ng wani shiri ne da ke kokarin tara kudade domin ciyar da ‘yan Najeriya masu bukata a lokacin kullen annobar COVID-19 ta hanyar hadin gwiwa, kamar yadda Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarni a irin kokarin da take yi na takaita yaduwar cutar a kasar.

Yi mana bayani kan abinda shirin Babban Gona ya kunsa

Babban Gona wani katafaren shiri ne jagaba a fannin habaka rayuwar al’umma a Najeriya da yake karkashin kulawar wani karamin rukunin manoma ta hanyar wani tsari da zai ja hankalin matasa.

Mambobin shirin za su sami horo ta bangaren ci gaba, bashi, kayan noma, tallafin tallata anfanin gonad a kuma sauran abubuwa.

Baya ga ninka amfanin da kowanne manomi ya ke samu a kowacce shekara tare da bunkasa kudin shigar kasa daga kimanin kaso 2.5 zuwa kaso uku, shirin na Babban Gona zai kuma yi aiki tukuru wajen ganin nuna cewa kananan manoma na da muhimmiyar rawar takawa a harkar zuba jari. Saboda haka muna fatan tara makudan kudade da za a yi amfani das u a mstayin jari a harkar.

Me ya karfafa gwiwarka tun da farko har ka yi tunanin kirkirar shirin?

Babban abinda ya karfafa min gwiwa na kirkiro shirin Babban Gona shine don in kare tabarbarewar tattalin arziki da kuma farfado da harkokin noma wanda zai samarwa da matasanmu ayyukan yi.

Shin an sami nasarar cimma wannan burin?

Shirin Babban Gona ya tallafawa da kanana manoma sama da 65,000 a fadin kasa su habbaka amfanin da suke samu daga kaso 2.5 zuwa kaso uku, yayin da kuma mambobin shirin ke samun ribar sama da Dala biyu a kan kowacce Dala daya da su ka zuba jarinta.

Tun da aka fara shi, shirin Babban Gona ya noma fadin gonakin da ya kai kimanin hekta 55,000 da hadin gwiwar kananan manoma.

Bugu da kari, kokarin samar da nagartattun amfanin gona ga ‘yan Najeriya ya janyo mun sami kwangilar sarrafa masara domin amfanin gidajen gona.

Sama da mutum 280,000 sun amfana da kayan abinci mai kara lafiya da manoman Babban Gona su ka noma, ciki har da masara mai karancin sinadaran aflatoxin da bio- fortified.

A sakamakon haka, wadanda su ka amfana su ke yabawa da tallafin shirin na Babban Gona. Naomi Michael wata wacce ta amfana da shirin ta ce irin ingantaccen takin zamani da iruruwan da ta samu daga Babban Gona ba tare da bata lokaci bay a taimaka mata wajen samin rubanya ribarta da kaso uku.

Hakika, hakan ya kawo canji a hada-hadar kudinta, ta inda har ta sami damar biyan kudin makarantarta.

Wani shima da ya amfana da shirin, Jibrin Mohammed ya ce ya sami horo matuka daga masana a fannin noma don riba kan fasahar shuka ta zamani. Wannan tallafin hadi da igantattun iraruwan shuka, takin zamani da magungunan kwari da ya karba daga Babban Gona ya rubanya amfanin da ya ke samu har sau biyar a gonarsa.

Ko za ka iya yi mana bayani a kan hadakarku da Givefood.ng?

Mu na aiki da al’ummomi da dama a Najeriya lokacin da kalubalen cutar COVID-19 ya fara, inda mu ka fi mayar da hankali wajen magance kalubalen da su ke fuskanta.

Takamaimai, a matsayinmu na kungiya mun fahimci cewa akwai karancin wayar da kan jama’a akan ita kanta cutar a tsakanin mutanen al’ummomin da mu ke hulda da su.

A sakamakon haka, mun tallafawa abokan huldarmu ta hanyar buga fastocin wayar da kai kimanin 120,000 mu ka kuma rarrabawa kimanin yankuna 5,000. Mun kuma samar da sakon murya na kusan tsawon mintuna biyar a manyan harsunan Najeriya tare da yadawa manoma.

Abu na gaba da mu ka yi shine mun gano cewa mutanen da su ke zaune a wadannan yankunan ba su da kayan kariya daga cutar, musamman a yankunan da ba su samun tsaftataccen rowan sha. A kan haka mu ka yanke shawarar samar musu da sinadaran tsaftace hannu kimanin tirela daya da yawansa ya kai guda 150,000 kuma muka rabawa wadanna al’ummomin a jihohi biyar na Najeriya.

Mun kuma raba kayan abinci bayan gano cewa annobar ta yi matukar illa ga hanyoyin samun kudin jama’a. Mun yi amfani da fasahar zamani wajen raba dubban ton-ton na kayan abincin wanda mu ka shafe tsawon kwana uku mu na yi ga jama’ar.

Mun kuma sami nasarar hada kai da sauran abokan hulda wajen samar da sama da mutum 200,000 kunshin abinci, yayin da su kuma wasu masu aikin sa kai su ka rika sayen kayan abincin daga manyan shaguna su ka rika rarrabawa mutane a kauyuka.

A matsayinmu na kungiya, mun kirkiri shirin Givefood.ng wanda mu ka tallafawa iyalai da dama.

Ta yaya ka sami nasarar jawo hankalin abokan hulda da yawa su tallafawa shirin naka?

Givefood.ng shafi ne na tattaro kudade da aka gina shi a kan amintaka. Abokan huldar Givefood.ng na daya daga cikin amintattu a harkar tattalin arziki na bangaren gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu.

Fasahar zamanin da mu ka kirkira ta taimaka mana sosai ganin mutane sun ci gajiyar shirin yadda ya kamata. Mun sami nasarar nasarar tabbatar da cewa kaso 100 na abinda mutane su ka tallafa da shi an yi amfani da shi bangaren abinci. Abincin ya fi tsabar kudi tasiri saboda duk wata N100 da aka tallafa da ita, mun yi kokarin sayen abincin N120 da ita.

Ta yaya ka samu dammar shigar da bankin Sterling cikin shirin?

Bankin Sterling wani ginshiki ne da shirin Babban Gona ya yi amfani da shi a baya wajen tsara manufofi, kuma muna da kamanceceniya da su wajen ganin mun ciyar da kasa gaba. Saboda haka abu ne da yake a zahiri.

Shin ko za ka iya fada mana yadda alakarka da bankin Sterling ta kasance a shirin?

Bankin Sterling ya taka muhimmiyar rawa wajen wayar da kan jama’a a kan shirin Givefood.ng ta hanyar amfani da yawan abokan huldarsu da kuma ta tallata shit a hanyar kafafen sada zumunta daban-daban.