Sterling Bank ya gano damar harkokin kasuwanci iri-iri bayan wucewar COVID-19 

Bankin Sterling Bank Plc, na Najeriya babban bankin kasuwanci ne a Najeriya, kuma ya gano dama iri-iri ga abokan huldarsa da za su yi amfani da su wajen cimma bukatunsu a sassa da dama na tattalin arziki bayan wucewar cutar -COVID-19. Manyan shugabannin zartarwar banki ne suka gano wadannan damarmaki a ci gaba da taron ganawa […]

Sterling Bank ya gano damar harkokin kasuwanci iri-iri bayan wucewar COVID-19 

Babban Daraktan Harkokin Kasuwanci na Bankin Sterling Bank, Tunde Adeola

Bankin Sterling Bank Plc, na Najeriya babban bankin kasuwanci ne a Najeriya, kuma ya gano dama iri-iri ga abokan huldarsa da za su yi amfani da su wajen cimma bukatunsu a sassa da dama na tattalin arziki bayan wucewar cutar -COVID-19.

Manyan shugabannin zartarwar banki ne suka gano wadannan damarmaki a ci gaba da taron ganawa da jama’a ta Intanet/webinar da Rukunin Sashin Kasuwancin na Bankin (Shiyyar Gabas) ya gudanar a kwanakin baya.

Babban Daraktan Harkokin Kasuwanci na Bankin Sterling Bank, Mista Tunde Adeola wanda ya karbi bakuncin taron ne ya gabatar da jawabin maraba ga mahalarta da masu tsara shirin.

Wadanda suka saurari ganawar sun hada da abokan hulda da na harkokin kasuwancin banki da suka fito daga Kudu maso Gabas da Tsakiyar Yamma da Kudu maso Kudu, wadanda suke taka rawa a sassa da dama na tattalin arzki da suka kama daga harkokin kasuwanci zuwa kiwon lafiya da noma da ilimi da sana’anta kayayyaki da harkokin man fetur da gas da sufuri da gine-gine da sauransu.

Da yake magana kan kiwon lafiya da sababbin dama iri-iri a harkokin ilimi, Shugaban Shiyya na Kiwon Lafiya da Ilimi na Bankin Sterling Bank, Mista Obinna Okakchukwu, ya ce, tsarin ilimi na Najeriya zai yi matukar canjawa bayan wucewar cutar COVID-19 ganin yadda ta bayar da dama da dama ta samun ilimi ta Intanet.

Ya ce nan gaba za a bukaci a samar da wani bangare a tsarin ilimi da zai kunshi koyarwa ta Intanet ta yadda yara da dalibai za su iya koyon ilimi ta kallon bidiyon koyar da ilimi ta Intanet yau da gobe.

Ya ce, malaman makaranta da suke koyarwa lokacin da ba a makaranta za su taka rawa a wannan yanayi, don haka akwai bukatar a yi tattalin samar da lakcarori da za su koyar ta hanyar fasahar zamani don bayar da damar karfafa tsarin ilimi ta Intanet.

Ukachukwu ya kuma yi magana kan sauran damarmaki inda ya ce akwai yiwuwar samun dama iri-iri wajen hadin gwiwa da sauran cibiyoyin ilimi don karfafa gasa da kuma inganta ayyuka a kokarin samun kudade.

Shugaban Shiyyar ya shaida wa mahalartar cewa bankin zai samar wa abokan huldarsa damar samun kudaden da za su ba su ikon cimma cikakkun damarmakin canjin da za a samu a bayan farfadowa daga cutar COVID-19.

Ya shawarci kamfanonin harhada magunguna su dada zuba jari wajen samar da magunguna tare da inganta abubuwan da asibitoci ke bukata da bude wuraren adana bayanai na Intanet (EMR) tare da tilasta wa asibitoci aiki da EMR, saboda asibitocin da ba su da EMR suna iya rasa majinyatan da za su rika zuwa musu.

Ukachukwu ya kuma shawarci jama’a su saukar da fasahar Tremendoc App, ta kiwon lafiya don su rika tuntubar likitoci kan kiwon lafiya ta Intanet, inda ya nuna bukatar da ke akwai ta samar da kudaden gudanar EMRs.

A jawabin, Misis Bukola Awosanya, Shugabar Rukunin Sashin Aikin Gona da Albarkatun Kasa na Bankin, wadda ta yi magana kan damarmakin samar da kudin aikin gona da kasuwancin amfanin gona, ta ce ’yan Najeriya za su iya bunkasa samar da abin da za su ci, inda ta ce bankin Sterling Bank yana da duk abin da ake bukata don tallafa wa manoma da sauran masu ruwa-da-tsaki a dukkan sassan harkokin noman.

Ta ce, yawan jama’ar kasar nan da kuma fadin kasar noma mai kimanin hekta miliyan 98.2 manyan damarmaki ne, sai dai ta nuna alhininta kan yadda noman rani bai taka rawar gani, lamarin da ke jawo kasar nan ke kashe kimanin Naira biliyan 25 wajen shigo da abinci daga waje.

Misis Awosanya ta ce akwai dimbin damarmaki na yin noma a Kudu maso Gabas na kasar nan, domin yananyin kasar da ke yanki za ta karfafa samar da kayan amfanin gona na sayarwa kamar yazawa da kwarar manja wadanda ake matukar bukata a kasuwannin waje.

Ta ce, yankin zai iya samar da dama sosai ta noman shinkafa da zazzabe ta da kuma gudanar da manyan gonakin kasuwancin da suka hada da noman rogo don fita da shi waje da kuma amfani da shi a gida ko amfani da shi a masana’antu don yin sitaci. Ta kara da cewa damar sarrafa koko don yin kayan abinci tana nan sosai a yankin.

A cewarta, yankin yana kuma da wasu damarmaki na kiwon kaji don samar da nama da kwai da kuma kasuwancinsu.

Misis Awosanya ta ce bankin ya samar sito-sito a sassan kasar nan don ba manoma damar adana kayayyakinsu su karbi rasidai wadanda za a iya mayar da su kudi kuma su sayar da su lokacin da suka ga dama.

Ta kuma yi magana a kan tsarin noma mai kawo riba da sauran harkokin noma da suka hada da kasuwancin amfanin gona ta Intanet da warware matsalar kudi da bankin ya samar don cimma bukatun abokan hulda masu zuwa da wadanda ake da su a shiyyar.

Mista Nyong Inwang na Sashin Mu’amala da Bankuna na Bankin Sterling Bank, wanda ya yi magana kan damarmakin Samar da Kudi, ya karfafa wa dillalai da masu samar da kayayyaki da suke hulda da bankin su yi amfani da wadannan damarmaki don cimma bukatun da ake so.

Ya ce, tsarin rarraba kudi na dillalan bankin yana ba abokan hulda jari ko hadin gwiwa don su samu nasarar cimma wadannan damarmaki tare da ba su damar samun kudade cikin sauri cikin awa 72 da za su kai har Naira miliyan 500 bisa kudin ruwa mai sauki da kuma bayar da rance ta hanyar Intanet (Specta).

Shugabar Sashin Tattara Bayanan Kudade na Bankin Sterling Bank, Abidemi Asunmo, wadda ta yi magana a kan Mafita da Damarmakin Amfani da Sadarwar Zamani, ta nuna alfanun bukatar amfani da fasahar sadarwar zamani da amfani da abin da zamani ya zo da shi a duniya da salon kula da asusun abokan hulda da yadda za a biya abokin huldar banki cikin sauri da amfani da bidiyo ko gani keke-da-keke kan yadda za a cimma buktatun abokan hulda.

Ta ce, akwai bukatar a samar da kayayyaki na zamani, saboda fasahar zamani za ta rage kudin da ake kashewa wajen gudanar da ayyuka, inda ta lissafo wasu biyan kudi ta fasahar zamani da suka hada da Sterling Pro da Cash collection solutions da PayOn da OneCollect da kuma Farepay domin saukin biyan kudi a cikin motocin bas-bas na sufuri BRT.

Basheer Oshodi, Shugaban Rukunin Zuba Jari na NIB Inbestments and Products na Bankin Sterling Bank, ya yi magana ce kan Wasu Sababbin Damarmakin Kudi da kasuwancin ta Intanet, inda ya ya ce jari da bashin duk an tsara su ne a ingantaccen tsarin harkokin kudi.

Ya ce, kayayyakin da za a yi kasuwancinsu wasu muhimman bangarori ne na sabuwar damar samun kudi, inda ya ce abokin hulda kan iya sake samun kudi kuma ya maye gurbin kadarori tare da shiga harkar hada hannu a cikin sauki.

Mista Chucks Aghaunor, Shugaban Sashin Tsara Kasuwanci da Samar da Kudin Fito na Bankin Sterling Bank, ya yi magana ce kan damarmakin fiton kaya zuwa kasashen waje da suka kunshin fita da kayayyakin da ba fetur ba da asusun fitar da kaya waje da tsarin fitar da kayayyakin da ba na kasuwanci ba da wasu kayayyakin da ake cin riba kamar kiraga da koko da yazawa da wayoyin alminiyom da tsofaffin karafa da kayayyakin hada magunguna da man girki da kwarar manja da manja da kayan marmari da doya da ma’adinai da sauransu.