….Su ne ke neman kashe jam’iyyar APC a Najeriya – Saleh Barde

  Wani dan fafutikar tabbatar da adalci a tsakanin al’umma mamba a jam’iyyar APC reshen jihar Bauchi Alhaji Saleh Barde ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya dauki mataki tun lokaci bai kure ba wajen taka birki ga gwamnonin da suke neman lalata jam’iyyar APC a jihohi da dama na kasar nan.  Matukar shugaba […]

….Su ne ke neman kashe jam’iyyar APC a Najeriya – Saleh Barde

 

Wani dan fafutikar tabbatar da adalci a tsakanin al’umma mamba a jam’iyyar APC reshen jihar Bauchi Alhaji Saleh Barde ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya dauki mataki tun lokaci bai kure ba wajen taka birki ga gwamnonin da suke neman lalata jam’iyyar APC a jihohi da dama na kasar nan. 

Matukar shugaba Buhari bai sa baki ba game da yadda abubuwa ke tafiya a jam’iyyar bana tsammanin cewa APC za ta kai 2018 mafi yawan wadanda suke cikin jam’iyyar za su sauya sheka zuwa wata sabuwar jam’iyya.
Da yawa daga cikin cikin gwamnonin APC an zabesu ne sakamakon shiga rigar Buhari da suka yi a zaben 2015.
Amma yanzu kan talakawa ya waye babu wanda zai sake shiga rigar shugaban kasa ya yaudari talakawan kasar nan sai mutum ya nuna gudunmawar da ya bayar ga al’umma kafin a kada masa kuri’a a 2019.
Watannin baya gwamnatin tarayya ta bada kudi naira biliyan-10 ga jihohin da suke fama da matsalar albashi daga bisani aka sake basu naira biliyan 20 amma har yanzu wasu daga cikin jihohin sun gagara biyan ma’aikatan jiha da na kananan hukumomi albashinsu.
Kamar yadda gwamnoni suke tunkaho a jihohinsu su ne shugabannin jam’iyya haka shugaban kasa shine shugaban jam’iyya a siyasan ce saboda haka wajibi ne ya bincike gwamnonin kudaden da ya basu domin su warware matsalar albashi me suka yi da kudaden.
Alhaji Saleh ya bayyana haka ne lokacin da yake amsa tambayoyin wakilinmu a ofishinsa dake Bauchi ranar litinin din makon jiya da yamma kuma ina tabbatar maka da cewa matukar haka gwamnoni za su cigaba da tafiyar da APC a jihohinsu.
To tabbas zaben 2019 talakawa za su iya tawaye ga APC tun daga sama har kasa don haka ayi gyara tun lokaci bai kure ba inji Saleh Barde.