Su Sambo manya!

Babu wanda ya yi mamakin irin halin da tsohon mai bai wa tsohon Shugaba Goodluck Jonathan shawara game da harkokin tsaro, wato Kanar Sambo Dasuki Mai Ritaya ke ciki a halin yanzu, domin kuwa shukar da ya yi ce yake girbar abarsa. An dai ce wanda duk ya sai rariya ya san za ta zubar […]

Su Sambo manya!
Su Sambo manya!

Babu wanda ya yi mamakin irin halin da tsohon mai bai wa tsohon Shugaba Goodluck Jonathan shawara game da harkokin tsaro, wato Kanar Sambo Dasuki Mai Ritaya ke ciki a halin yanzu, domin kuwa shukar da ya yi ce yake girbar abarsa.
An dai ce wanda duk ya sai rariya ya san za ta zubar da ruwa, shi ya sa yadda Kanar Sambo ke kwance bisa gadonsa daidai da yadda ya yi shimfidarsa ne. Muhimmin aikin da tsohon Shugaba Goodluck Jonathan ya dauki Kanar Sambo Dasuki don yi masa shi ne ba shi shawara game da harkokin tsaro, amma da yake da ma can  ana so ne a samu wani kasurgumin dan koren Yahudawa, wanda zai juya wa jama’arsa baya, ya kuma nuna tsananin kiyayya ga matsayinsu da kuma abin da suka yi imani da shi, sai ga shi nan  Kanar Sambo ya wuce gona da iri, ya shiga harkokin siyasa tsundum, yana daukan munanan matakan ganin ubangidansa ya zarce bisa mulki a karo na biyu don a ji dadin ci gaba da aiwatar da miyagun manufofin da za su muzgunawa al’ummomin  wani  bangaren kasar  nan.
Dangane da haka Kanar Sambo ya taka rawar da kowa ya yi Allah-wadai da ita a dambarwar da ake yi don murkushe ‘yan ta’addan kungiyar Boko Haram, wacce aka zargi manyan hafsoshin rundunonin mayakan kasar nan da  kasa yin wani takabus don murkushe su, da kuma ingiza wutar rikicin da ya-ki-ci-ya-ki cinyewa, abin sai ka ce cin kwan makauniya, bayan makudan kudade na fitar hankali da aka yi ta antaya masu don sayen makamai da kayayyakin aiki. An tabbatar da cewa babu wata kirar da wadancan   manyan hafsoshin rundunoni suka yi, amma babu gawayin da aka tanada don yin kirar.  Hasali ma dakarun Najeriya nokewa suke yi sa’ilin da ‘yan ta’adda suka kai masu farmaki, domin kuwa ba za su iya fuskantar su ba saboda sun fi su ingantattun makamai irin na zamani da sauran kayayyakin aikin da ba su da su.
Kurar Sambo Dasuki dai ta yi kuka dangane da lusarancin manyan kwamandojin  rundunonin sojoji wadanda suka sayar da lafiya, suka sayo cuta, sa’ilin da ya yi masu jagorancin daurewa karya gindi har suka gwammace goyon bayan ubangidansu, Goodluck Jonathan don  samun nasara a zabe. A lokacin ne  Kanar Sambo ya yi takakka har zuwa Birnin London, bayan ya fahimci cewa keyar Jonathan za ta sha dasa a zaben, don  yi wa hukumar zabe sharri a wata laccar da ya gabatar a wani mashahurin wurin taro da ake kira Chatham House,  cewa ba ta shirya wa zaben ba saboda haka nan sai a dage shi zuwa wani lokaci idan ta kammala shirye-shiryen da suka kamata don samun nasara.  
Daga bisani  majalisar tsoffin kasa da gwamnonin jihohi da kuma tsoffin manyan alkalan kasar nan suka yi wani muhimmin taro, suka kuma shawarci hukumar zabe ta ci gaba  da tsarin gudanar da zaben tun da dai an fahimci cewa ta shirya tsaf dangane da haka. Amma daga bisani sai Kanar Sambo Dasuki ya kukuta, ya hurewa wadancan kwamandojin askawaran kunnuwa, har suka fito karara, suka ce kasar ba ta zaune lafiya, kuma ba za su samar da ingantaccen tsaro ba a lokacin da aka shirya gudanar da zabe, saboda haka nan sai a daga kamar yadda Kanar Sambo ya nema. Kuma haka din  gwamnatin Jonathan ta yi don a bayar da damar kitsa munakisar da za ta sanya ya haye cikin ruwan sanyi.   
To da yake an ce alhaki kwuikuyo ne sai ga shi nan yana ta bin Kanar Sambo Dasuki, kuma shi da abokan kitsa kutungwilarsa suna ji, suna gani, wanda suka yi wa kafar angulu ya tsallake rijiyar da suka haka masa da baya. An  wancaklar da su Sambo, amma ba su ga kwanciyar hankali ba, kuma kaman sun hadiya tabarya, tun daga wancan lokacin a tsaye suke, ki-kam kaman falwaya, ba su ga ta zama ba.  Hukumar tsaron farin kaya, DSS ta ce ma’aikatanta sun bankado wani shirin Kanar Sambo da suka ce wai yana shirin yi wa gwamnatin kasar nan wata munakisa ko makarkashiyar da za ta gurgunta ta. A sakamakon haka ne aka bidi a yi cikakken binciken hujjojin da jami’an tsaron suka yi zargin cewa suna nan jibge a gidajensa da ke Abuja da kuma gidan mahaifinsa da ke Unguwar Gwiwa a Sakkwato.
Jami’an tsaro sun dumfari gidan Kanar Sabo da safiyar Juma’a, ranar Salla karama, don aiwatar da binciken, rike da takardar iznin yin haka da wani alkalin babban kotun Abuja ya sanya wa hannu, amma sai Kanar Sambo ya ki amincewa da haka, ya kuma umurci sojojin da ke gadin idansa ba bisa ka’ida ba, da su dirka wa  wanda duk ya gwamatsi gidansa bindiga  da niyyar gudanar da binciken. Haka nan aka yi ta gwa-gwa-gwa na kusan awanni goma kafin sojojin da ya gayyato bisa zargin da ya yi cewa ga wasu nan sun mamaye gidansa suka zo, suka kuma fahimci cewa ashe dai zuki-ta-malle ce ya shara. An kutsa gidan, an kuma gudanar da bincike, daga bisani jami’an tsaro sun kwashi wasu tarkace, ciki har da kwakwalwar wani komfuta, da suka tabbatar za su iya kalatar  bayanan da suke nema. Sun kuma yi awon gaba da wasu motocin alfarma, masu dan karen tsada, guda bakwai da ya kasa gabatar da shaidar mallakarsu, suka kuma kwashi wasu zabga-zabgan bindigogi guda bakwai, da ma’ajiyar harsasai guda ashirin, da tsabar kudi har dala dubu arba’in, kwatankwacin miliyan goma a karkashin matashin kansa.
Sauran bayani kuma game da sakamakon binciken ko  makomar Kanar Sambo zai biyo baya, kuma kowa abin da ya kasa kunne ke nan ya ji, musamman ma zargin da wata jarida ta yi cewa shi Kanar Sambo ne kan gaba wajen shigo da sojojin haya daga kasashen makwata masu  kai wa bayin Allah farmaki da sunan Boko Haram. Yanzu dai Kanar Sambo Dasuki ya ce wannan abin da aka yi masa cin mutunci ne da ba zai iya kyalewa ba, saboda haka nan zai garzaya kotu don a bi masa hakkinsa, to amma sauran jama’ar da suka tagayyara sakamakon aikace-aikacen da ake zarginsa na cewa  ai sai ya yi maza, kada kuda ya riga shi. Su Sambo manya! To Allah Ya sa idan ya je kotun  kada allura ta tono garma.