Su wa ye asirinsu bai tonu ba?
Daga Yasir Ramadan Gwale Allah Ya tona asirin azzalumai, mai aikata miyagun laifuka, tamkar yadda ’yan Najeriya ke ta rokon Allah. Abin kawai ya rage mana mu roki Allah ya ba mu ikon hukunta su. Shin akwai wasu barayi a Najeriya manya da kanana da ba’a sansu ba? Ana t akafa kwmaitoci, wadanda sakamakon bincikensu […]
Daga Yasir Ramadan Gwale
Allah Ya tona asirin azzalumai, mai aikata miyagun laifuka, tamkar yadda ’yan Najeriya ke ta rokon Allah. Abin kawai ya rage mana mu roki Allah ya ba mu ikon hukunta su. Shin akwai wasu barayi a Najeriya manya da kanana da ba’a sansu ba? Ana t akafa kwmaitoci, wadanda sakamakon bincikensu ba a amfani d ashi, illa kawai a karshe aga ya wuce tamkar tafiyar ruwa.
Shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan da kansa ya ce yasan duk barayin man fetur, shin ba ALLAH ba ne ya tona wa shugaban kasa asiri ya yi wannan furuci? Shugaban ya taba fada cewa a cikin gwamnatinsa akwai ‘yan Boko Haram, Marigayi tsohon mashawarcin kasa kan harkar tsaro janar Azazi da kansa ya ce ‘PDP su ne Boko Haram,’ shi ne masanin dukkan wasu rahotannin tsaro na sirri, shin ba ALLAH ba ne ya tona masa asiri ya yi wannan furucin ba? Yanzu su waye suka rage asirinsu bai tanu ba? Duk inda ake saida giya da masu shan giyar an sansu, an san masu yin zina da luwadi da madigo da dukkan ayyukan badala an san su, suma masu aikatawar sun san angane su, amma saboda an san duk ba gaskiya garemu ba, shi yasa babu wanda yake jin kunyar aikata ba daidai ba!
A karshen shekarar 2011 aka kama wata mata Lucy Danaga Kirista ta yo safarar makamai a cikin buhunhunan hatsi zuwa jihar Adamawa, ALLAH ya tona asirinta aka kamata, shin me aka yi tun daga wancan lokaci zuwa yanzu? An kama wasu batagari kiristoci su takwas a kauyen Miya Barkate Jihar Bauchi da yunkurin tayar da Boma-bomai a coci, shin me aka yi tun a wancan lokaci zuwa yanzu? A Jihar Bayelsa an kama wani Kirista da shiga irin ta Musulmi ya yi yunkurin tayar da Bom a coci, shin me aka yi masa? A jihar Fulato an kama kwanturola na kwastan da yin safarar makamai zuwa ga ‘yan kabilar Berom, shin me aka yi masa? A dai Jihar Fulaton kuma aka kama wani kirista, wanda ya tayar da Bom a COCIN CHURCH, wanda dukkan bayanai suka tabbatar da cewa cocin da ya kai hari a nan yake zuwa yin ibada, shin me ya faru?
Idan muka koma batun cin hanci da rashawa mutum nawa EFCC ta kama da laifin satar dukiyar jama’a? Ina Saminu Turaki da ya saci Biliyan 38? Ina Gwamna Alams na Bayelsa, da Gwamna Lucky Igbenedion na Edo, da Danjuma Goje na Gombe, da Aliyu Akwe Doma na Nassarawa da sauran tsofaffin gwamnoni da dama; shin Allah bai tona musu asiri ba? Abin mamaki Kotu a England ta yi wa tsohon Gwamnan Delta James Ibori hukunci, saboda ya yi wa ‘yan Najeriya sata ba ‘yan Birtaniya ba! Shin babban bankin Najeriya bai bankado badakalar bankuna da dukiyar jama’a ba? Ina batun badakalar Halliburtun, da Baswani Brothers, da Siemens, da Fanshon ‘yan Sanda? Duk wadannan Allah bai tona musu asiri ba, uwa uba ina batun mutanen da rahoton Hon Farouk Lawan ya bankado da ci da gumin talaka na kusan Naira Tiriliyan daya, Ina batun rahoton kwamtinin Nuhu Ribadu da aka bankado sama da fadi ta kusan Tiriliyan biyu? Duk wadannan ba ALLAH bane ya tona musu asiri?
Mun gani a kasar Birtaniya saboda mutanen gaskiya ne, rayuwar gaskiya ake yi Tony Blair bai kai karshen wa’adin mulkinsa ba ya sauka, Gordon Brown shi ma bai tumma wa’adinsa ba ya san inda dare ya yi masa, saboda sun aikata ba daidai ba; Sulbio Baluskoni a Italiya shi mai bai karasa wa’adinsa ba, har kotu ya je duk saboda al’ummarsu da gaske suke, don haka babu yadda Nanun za ta ci su, alhali ba su ci ba.
‘Yan Najeriya da suke neman ya tona wa dukkan batagarin al’umma asiri. Yanzu kawai abin da ya rage shi ne, wane shiri al’ummar Najeriya suka yi na tunkarar wadanda Allah ya bankada asirinsu, ko kuwa shi ke nan idan asirin mutum ya tonu ya wadatar? Yanzu muna cikin halin ga barawo kuma ga mai Kaya ne! Amma barawon yasan mai kayan mutumin banza ne babu abin da zai iya yi masa, shi ma mai kayan yasan ba da gaske yake ba. Don haka barayi da miyagu suke watayawarsu yadda suka ga dama, suna yake hakora a wajen taruka kamar ba su aikata komai ba. Dukkan wata mafita da makoma sahihiya da mu ‘yan Najeriya wadanda aka zalunta aka sace mana dukiya, aka kashe mana ‘yan uwa, mafitar tana hannunmu, wadanda suke ikirarin su ne Shugabanninmu, babu wani abu da za su iya yi, domin ko dai su na daga cikin wadanda Allah ya tona wa asiri, ko kuma an sata an ba su ladar ganin Ido, ko kuma suna gani ana satar suka kawar da kai.
Idan da da gaske hukumomi suke son gyara tabbas da an yi. Dukkan wani abu da ya kamata a fada dangane da gyaran kasar nan an fade shi, duk wani rubutu da ya kamata a yi an yi shi, kusan duk wani abu da za a yi maimaitawa kawai ake yi, barayi ne kawai ke samun ci gaba daga satar miliyan zuwa Bilyan har zuwa Tiriliyan. Ina kwamitocin da aka kakkafa, ina rahotannin da suka bayar? Ina kwamitin Mai Shari’a Uwais, da Kwamitin Alfa Balgore, da Kwamitin Shehu Lemu, da Kwamitin Giltimari da sauran kwamitoci da aka kakkafa, domin bayar da shawarar yadda za a kyautata lamura, duk sun yi rubutu sun bada dukkan irin shawarwarin da ake bukata da kuma mafita, amma ina suka shiga? Muna tsammanin wadannan gungu na miyagu azzalumai ne zasu kawowa rayuwarmu sauyi?
A lokacin da aka nada Attahiru Jega a matsayin sabon Shugaban Hukumar Zaben, Gidan Mumbayya sun shirya wata tattaunawa mai suna “Path way to the credible election, wato tafarkin yin zabe mai inganci” inda Farfesa Alkassim Abba na Jami’ar Jihar Adamawa da ya gabatar da kasida, ya yi bayanin duk irin yadda lamura suka tabarbare, ba na mantawa wani dalibin jami’a ya yi tambayar mece ce mafitar halin da muke ciki?! A lokacin Farfesan ya ba shi amsa da cewa mafita tana hannunka da kai da sauran abokanka, da dama mun dauka cewa bakar magana ya fada masa. Amma yanzu tabbas na gama gamsuwa cewa mafitar duk wannan halin da muke ciki tana hannunmu. Yanzu zabi ya rage ni da kai da sauran al’umma wadanda aka zalunta, mu taka wa abin burki. Domin duk wadannan masu aikata laifukan ba za su daina ba, kuma ba za su taba jin kunya ba, domin waliyyan shaidan ne, shi yake yi musu wasiyya da aikata laifuka, tunda suka kafirce wa Allah, dole su yi wa shaidan biyayya. Abu ne a bayyane, amma wa ye ya isa ya ce Uwar Sarki Mayya ce?! Shi ne inda gizo ke sakar. Allah ka ba mu ikon daukar mataki akan miyagun mutane, wadanda suka cuce mu.
Yasir Ramadan Gwale