Su wane ne mayaudaran Arewa?
Bahaushe kan ce dadinsa da gobe saurin zuwa. Kwanci-tashi ga wani lokacin sake zaben shugabanni da ‘yan majalisu ya kusan karatowa, kuma talakawan da aka sha su ba su warke ba, suna ta cizon yatsa saboda zambatar da shugabanninsu ke yi masu a irin wannan lokacin, har yanzu ba su dan dara ba, suna nan […]
Bahaushe kan ce dadinsa da gobe saurin zuwa. Kwanci-tashi ga wani lokacin sake zaben shugabanni da ‘yan majalisu ya kusan karatowa, kuma talakawan da aka sha su ba su warke ba, suna ta cizon yatsa saboda zambatar da shugabanninsu ke yi masu a irin wannan lokacin, har yanzu ba su dan dara ba, suna nan manne da su, suna kokarin sake cin tuwo da miyar jiya. Da zarar an kammala zaben da aka kada wa talakawa wala-wala sai ka ji suna cewa an ci kubeji, daga wannan ba za a kara ba, amma sai a ci gaba da gasa masu aya a hannu. A takaice dai a kullum talakan Najeriya, musamman na yankin Arewa kara dimaucewa yake yi, shugabanninsa kuma a ko da yaushe kara kwarewa suke yi wajen yaudararsa da kuma gano sababbin dabarun dulmuya shi cikin matsalar da zai kasa ficewa.
Shugabannin Arewa sun mayar da talaka dokin sukuwarsu, wanda bai san ciwon kansa ba, ba shi kuma da halin fahimta ko nakaltar hanyar da ake bi ana cutarsa, kuma ko da ma ya gane, ba shi da ikon kauce wa tarkon da ake dana masa. Dalili kuwa shi ne shugabanninsa sun rigaya sun sayar da mutuncinsa, sun karbi awalajar, kuma la’ada waje. Wadannan shugabannin duk sun rikide ‘yan koren makiya Arewa da abin da ‘yan Arewa suka dogara da shi ko imani a kansa; babu abin da ya dame su sai yadda za a hada baki da su a cuci Arewar, sa’annan daga bisani su fi kowa nuna damuwarsu da haka, suna ta kwakwazo cewa an cuci mutanensu.
Da farko dai wasu fitattun ‘yan Arewar ne da suka kai kololuwar mukami a gidan soja suka zubar da mutuncin yankinsu, suka kuma wargaza hadin kan jama’arsu ta hanyar samar da wata dama ta musamman ga tsirarun kabilun Arewa, har suka hada kai da makiyan Arewan daga yankin Kudu da niyyar kifar da Arewar, a kuma dakile jama’arta. Wannan ne ya kawo siyasar kabilanci da tsananin gaba tsakanin al’ummomin Arewa da na Kudu. Daga bisani ne kuma wasu gafalallun ‘yan siyasar Arewa suka yi amfani da addini domin rarraba kawunan Musulmi da Kiristocin Arewa wadanda kafin wannan lokaci suke zaman lumana da fahimtar junansu, ba kamar yanzu ba da ake sama-sama suke, wai zaman doya da manja.
A dukkan lokutan da ake daukar matakan farraka kan al’ummomin Arewa sai an samu hadin kan shugabannin yankin wadanda kan fake da guzuma, su harbi karsana, watau su nuna suna tare da jama’arsu, amma kuma suna yi masu yankan baya da kuma bude kofar da za a kai ga dakile burinsu.
Shi ya sa a dukkan lokutan da zaben shugaban kasa ya kusanto wadannan shugabannin za su bullo da sababbin dabarun kawar da hankulan talakawa daga kudurinsu na zaben wanda zai jagorance su zuwa tudun-mun-tsira, a nuna musu wata manufa can ta daban wacce daga karshe ba za ta biya bukatarsu ba. An dai ga yadda suka yaudari ‘yan Arewa a shekarar 1999, suka taimaka wajen fitar da ‘yan kudu guda biyu don takarar shugabancin kasa, suka kuma daure wa gudansu gindi, ya yi mulkin da ya ba shi damar durkusar da Arewar da kuma dukkan ‘ya’yanta da suka taba yin cara a fagen siyasa ko na mulkin soja. Wanmnan ne matakin farko na daidaita Arewa, kuma akansa ne makiyanta ke dorawa yanzu.
To ga shi nan tun kafin jam’iyyu su fara batun fitar da ‘yan takarar shugabancin kasa, an bullo da wasu sababbin kungiyoyi da zimmar hada kan Arewa da taimakon wadancan manyan dattijan da ake ikirarin kishin Arewa, don a ci gaba da yaudarar ‘yan Arewa su amince da wani can wanda bai kaunarsu da kuma ci gaban yankinsu. Daga cikin wadannan kungiyoyin babu guda daya da ke tare da talakawa, ko kokarin tallafa wa wanda talakawan Arewa ke son sanya wa a gaba; hasali ma bakar gaba da suke yi da irin wannan mutumin, suna kokarin kwashe masa kafa, ko su taimaka wajen shafa masa kashin kaji don kada ya yi wani tasiri idan jama’a suka nuna shi a matsayin gwarzonsu.
Idan har da gaske ne wadancan kungiyoyin ke yi wajen daukaka matsayin Arewa da kuma dawo mata da martabarta, me ya sa ba su dunkulewa waje guda, su lalubo mutum daya da ya fi su kishin Arewa, su ba shi goyon bayan tsayawa zabe da kuma taimaka masa don ya haye? Ina za su yi haka, bayan suna karbar kudin Yahudu na Nasara don yi masu hidima? ‘Yan Arewa su yi nasara wajen haurowar mulki yankinsu muddin bakunan wadancan shugabannin ba su zo daya ba, ba su kuma komo daga rakiyar masu kokarin ci gaba da farraka kawunan ‘yan Arewa don a ci gaba da mayar da su ‘ya’yan bora a kasar da suke da cikakken ‘yanci kamar kowa. Muddin ba tsofaffin janar-janar din kasar nan da kuma fitattun ‘yan siyasan yankin Arewa da manyan malaman addini sun hada karfi da karfe ne wajen fafutikar tserar da Arewa daga kangin makiyanta ba, to kuwa babu ranar da tsuguni-tashi za ta kare a yankin. Ya kamata a ce a yanzu ‘yan Arewa sun fahimci ko su wane ne ke yaudararsu, su kuma gina katangar karfe tsakaninsu.