Sudais ya bai wa Mahir hutun limanci a Masallacin Harami

A jiya Juma’a ne dai Seikh Maher ya fadi lokacin da yake tsaka da karanta Suratul Fatiha.

Sudais ya bai wa Mahir hutun limanci a Masallacin Harami

Babban Limamin Masallatan Harami, Sheikh Abdurrahman al Sudais, ya bai wa Sheikh Maher Almu’aikali hutun limancin Sallar Asuba da Azahar a ranar Asabar sakamakon suma da ya yi a jiya Juma’a yana tsaka da jan Sallar Juma’a.

Sudais ya kuma bai wa Maher din umarnin hutawa a gida, har zuwa lokacin da zai warke daga rashin lafiyar da ke damunsa.

A jiya Juma’a ne dai Seikh Maher ya fadi lokacin da yake tsaka da karanta Suratul Fatiha yayin Sallar Juma’a, inda sheikh Sudais ya yi wuf ya karbi jagorancin sallar.

Daga baya dai shafin Haramain Sharifain ya rawaito cewa Mahir ya samu sauki, amma ba zai iya karasa Sallar Juma’ar ba.

Uwargidan Sanata Goje ta tallafa wa mata da matasa a Gombe

An kama bokaye 2 kan zargin yi wa shugaban Zambiya asiri

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano

Gwamnatin Kano na shirin tara harajin 80bn a 2025