Sudais ya raba gora 40,000 ta ruwan Zamzam ga masu COVID-19
Yadda Masarautar Saudiyya ke kokarin samar da ruwan Zamzam a wadace
Kasar Saudiyya ta raba ruwan Zamzam fiye da gora 40,000 ga mutanen da ke fama da cutar COVID-19.
An raba ruwan Zamzam din ne a fadin kasar bisa umarnin Shugaban Limaman Masallacin Harami a Kasar Saudiyya, Sheikh Abdulrahman Sudais.
- Mai sayar wa ’yan bindiga babura ya shiga hannu a Kano
- Gwamnatin Kano za ta gurfanar da mawakin yabo, Bashir Dandago
- Yadda mutanen Jingir suka yi wa ’yan bindiga kofar rago
- Ramadan: An kaddamar da keken rabon ruwan Zam-Zam a masallatan Harami
Ruwan Zamzam, wanda ya samo asali tun zamanin Annabi Ibrahim (AS), a halin yanzu ana samun shi ne a Masallacin Haramin Makkah kuma yana da matukar falala da daraja a wurin al’ummar Musulmi.
Daga cikin falaloin ruwan na Rijiyar Zamzam wadda ta samo asali dubban shekaru da suka gabata, Hadisan Manzon Allah (SAW), sun tabbatar cewa magani ne ga cututtuka.
Ci gaban zamani ya sa Masarautar Saudiyya amfani da kimiyya wajen inganta samar da ruwan ta bakin famfuna da aka jawo daga rijiyar a harabar Masallacin, cikin cikakkiyar tsafta da matakan kare lafiya.
An kuma sanya ruwan a cikin mazubai na musamman iri-iri don saukaka samun sa ga masu ibada.
Ko a makon da muke ciki, Sheikh Sudais ya kaddamar da kekuna na musamman masu dauke da ruwan Zamzam da kuma famfuna domin jigilar ruwan a harabar Masallacin Haram.
Wannan kari ne a kan jakkunan baya na musamman da aka kaddamar a 2020 wadanda ma’aikata ke yawo da su suna raba wa masu ibada ruwan a goruna ko kofuna.
Akwai kuma randuna na musamman da aka tanadar dauke da ruwan mai sanyi da kuma madaidaici gwargwadon bukatar masu ibada a lunguna da sakon masallacin.