Sudan: An dage shari’ar juyin mulkin al-Bashir

Ana tuhumar tsohon shugaban na shekara 30 da rashawa da take hakki jama’a

Sudan: An dage shari’ar juyin mulkin al-Bashir

Omar Hassan al-Bashir, tsohon Shugaban Kasar Sudan, a lokacin da aka gurfanar da shi a kotu.

Kotu ta dage sauraron shari’ar tsohon Shugaban Kasar Sudan Omar Hassan al-Bashir kan juyin mulkin da ya kawo shi kan mulki, zuwa ranar 11 ga watan Agusta.

Bayan lauyoyi sun yi kokafin cewa wasunsu ba su samu shiga cikin kotun ba ne a ranar Talata kotun ta dage sauraron shari’ar domin a samu babban wurin da karin lauyoyi da iyalan wadanda ake zargi su samu damar halarta.

Gwamnatin Sudan ta fara gurfanar da al-Bashir ne bayan sojoji sun hambarar da gwamnatinsa sakamakon boren da ’yan kasar suka yi na nuna kin jinin gwamnatin tasa da ta yi ta mulki tun shekarar 1989.

Al-Bashir wanda ke tsare na fuskantar shari’o’i kan zarge-zargen cin rashawa da tauye hakknin jama’a da karya dokar kasa da kuma yi wa firai minista Sadiq al-Mahdi da ya kayar da shi a zabe juyin mulki.

Sojoji sun daƙile harin Boko Haram, sun ceto mutum 9 a Borno

’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 3 a Binuwai

Mahara sun sace bsarake, sun harbi matarsa a ƙauyen Ondo

Sarkin Musulmi ya umarci a fara neman jinjirin watan Muharram