Sudan ta ba Kano kyautar gurbin karatun likita 40

Gwamnatin kasar Sudan ta ba Jihar Kano gurbi 40 domin karo karatun aikin likita kyautaJakadan Sudan a Kano Sheikh Muhammad bin Uthman El-Tayyab ne ya bayyana haka a lokacin da ya kai ziyarar girmamawa ga Gwamnan Jihar Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso.Ya ce wadanda za su amfana da gurbin za su samu cikakkiyar kulawa a tsawon […]

Sudan ta ba Kano kyautar gurbin karatun likita 40

 Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso Gwamnan Jihar KanoGwamnatin kasar Sudan ta ba Jihar Kano gurbi 40 domin karo karatun aikin likita kyauta
Jakadan Sudan a Kano Sheikh Muhammad bin Uthman El-Tayyab ne ya bayyana haka a lokacin da ya kai ziyarar girmamawa ga Gwamnan Jihar Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso.
Ya ce wadanda za su amfana da gurbin za su samu cikakkiyar kulawa a tsawon lokacin da za su yi karatu a kasar wanda zai fara a shekarar karatu ta badi.
Jakadan ya ce Sudan ta ba fiye da daliban Jihar Kano 1000 gurbin karatu a kasarta sakamakon dadaddiyar danagantakar da ke tsakanin kasashen biyu. “Dangantaka tsakanin Najeriya da Sudan ta fara ne tun kafin zuwan Turawan mulkin mallak, kuma muna fatan dorewarta, ta yadda za mu yi aiki tare don amfanin juna.” inji shi.
A lokacin da yake mayar da jawabi Gwamna Rabi’u Kwankwaso ya nuna godiyarsa ga kasar Sudan saboda wanann abin alheri da take yi wa ’ya’yan Jiha Kano. “Wannan abin alheri da Sudan ta yi na ba ‘ya’yan Jihar Kano gurbin karatu kyauta a jami’o’in kasar abu ne da zai kara karfafa dangantakar kasashen biyu, musamman ta fuskar tattalin arziki.”  
Gwamnan ya ce “A koyaushe mutanen Sudan suna ganin Kano a matsayin gida, dubi da irin dadewar dangantaka a tsakanin kasashen biyu. Kuma tarihi ba zai mance da irin gudunmawar da mutanen Sudan suke bayarwa ga ci gaban tatatlin arzikin Najeriya.”