Sudan-ta-Kudu: Munafuncin Dodo yakan ci mai shi

Rikicin da ya barke a kasar Sudan-ta-Kudu makon jiya wata ‘yar manuniya ce da ta nuna alhaki kwiykwiyo ne mai shi yakan bi. Alama ce da ke nuna Sudan-ta-Kudu ta kama hanyar da za a ce sai buzunta, musamman ma da shugabanninta suka zama tamkar almajiran tsangaya da kowa allon da yake hannunsa yake biyawa, […]

Sudan-ta-Kudu: Munafuncin Dodo yakan ci mai shi
Sudan-ta-Kudu: Munafuncin Dodo yakan ci mai shi

Rikicin da ya barke a kasar Sudan-ta-Kudu makon jiya wata ‘yar manuniya ce da ta nuna alhaki kwiykwiyo ne mai shi yakan bi. Alama ce da ke nuna Sudan-ta-Kudu ta kama hanyar da za a ce sai buzunta, musamman ma da shugabanninta suka zama tamkar almajiran tsangaya da kowa allon da yake hannunsa yake biyawa, ba ruwansa da na wani. Shugabanni a kasar kowa na biye allon son zuciyarsa ne tare da burin ya haddace hade da ganin ya wanke allonsa wurin samun biyan bukatarsa da ta kabilarsa.
Rikicin da ya balle din na kabilanci ne wurin neman mulki tsakanin kabilar Nuer da ke goyon bayan Shugaban kasa Salba Kiir da kuma kabilar Dinka da ke goyon bayan Riek Marchar, tsohon mataimakin shugaban kasar.
A yayin rikicin an kashe dubban mutane, inda Larabar makon jiya wadansu mahara suka kutsa kai sansanin da majalisar dinkin duniya ta tsugunar da wadanda rikicin ya shafa, suka kuma kashe mutane da yawa. Majalisar dinkin duniya ta ce ana gab da fara yakin basasa a kasar.
Bayan an ji karar harbe-harben bindigogi a Juba, babban birnin Sudan-ta-Kudu Lahadin makon jiya, sai gwamnatin kasar ta ce tsohon shugaban kasar Marchar wanda suka raba gari da tsaba da Shugaba Kiir a watan Yulin da ya gabata ne ya kitsa kai hare-hare bayan ya shirya juyin mulki. Sai dai gwamnatin kasar ta ce Marchar bai samu nasara ba. Wata majiya ta ce shugabannin sun samu sabani ne sakamakon son zuciyoyinsu na mallakar madafun ikon kasar. Dangantaka tsakanin shugaba Kiir da tsohon mataimakinsa ta yi tsami, har suka raba gari. Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce, Shugaba Kiir na mulkin danniya da kama karya, inda kuma Kiir ya ce tsohon mataimakinsa ba shi da wani buri sai dai komai a ba ‘yan kabilarsa, inda ya ce mulki ba zai taba yiwuwa haka ba.
Idan ba za a manta ba dai ‘yan kabilar Dinka da Chol da Nuer da sauransu ne suka yi ruwa da tsaki bayan sun kai gwauro sun kai mari wurin samun ‘yanci daga Sudan. Wadannan kabilu sun samu goyon bayan Amurka da mukarrabanta ta hanyar amfani da majalisar dinkin duniya wajen yin uwa da makarbiya don ganin an raba Sudan da kuma Sudan-ta-Kudu, musamman ma ganin cewa Sudan-ta-Kudu akwai man fetur da idan hakar rabuwar ta cimma ruwa, to Amurka da ‘yan kanzaginta ne za su sha romon rabuwar, domin Sudan-ta-Kudu za ta zama tamkar biri a hannu Bamaguje, sun kuma yi irin abin nan da ake cewa kura da shan bugu gardi da kwashe kudi, ma’ana sun yi fafutikar kwatar ‘yancinsu amma ta wani hannu Amurka tana zuke arzikinsu. Amurka da jama’arta sun tabbata idan Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir na rike da madafun ikon kasar to kuwa man da ke kasar ya zama musu tamkar garin dadi na nesa da ungulu ta leka masai.
A takaice haka aka yaudare su, domin an yi musu romon baka da kururuwar cewa idan suka samu ‘yancinsu daga hannun Omar al-Bashir wanda a cewarsu ya zama musu gandagarki mugun shinge shi ke nan duniyarsu ta dawo sabuwa. Amma da yake ba su san tsiyar Nasara sai za shi gida ba sai suka ba da kai bori ya hau, wanda a yanzu suka fara gane an yi musu sakiyar da babu ruwa, domin idan har Omar ne matsalarsu da ba su afka cikin rikici ba.
Masu iya magana sun ce gani ga wane ya ishi wane tsoron Allah, kuma idan gemun dan uwanka ya kama wuta sai ka shafa wa naka ruwa. Abin da nake nufi a nan shi ne, masu kururuwar sai an raba Najeriya musamman ‘yan Kudancin kasar nan su gane hakan ba zai haifar mana da mai ido ba. Ina so a fahimci ruwa kawai ba ya maganin dauda, sai an hada da soso da sabulu, jama’a su gane babu wani yankin a Najeriya da yake da hannun da zai iya sosa kaikayin bayansa, sai ya bukaci taimako. Mu fahimci ba rabuwar ce za ta kawo karshen matsalolinmu ba, a’a, samun shugabanni nagari masu kishin kasa da talakawansu ne mafita. Domin a cikin shugabanninmu na Kudu da Arewa, Musulmi da Kirista,  Bahaushe ne, ko Ibo ko Bayarabe ne, babu wanda ya tabuka abin-a-zo-gani wajen kyautata rayuwar talakawan da yake mulki. Talauci ya habaka, cin hanci da rashawa sun yi kaka-gida, matsalar tsaro ta yi zaman dirshan, rashin aikin yi ya bunkasa, ilimi ya tabarbare, babu wani abu da yake motsawa a yanzu da ake yabawa.
Idan aka raba Najeriya babu yankin da babu manyan yaruka da kabilu, burin kasashen yammancin Turai kada sauran kasashen duniya su samu zaman lafiya, domin haka barazana ce gare su, domin ba za su ci gaba da mayar da kowa saniyar tatsa ba, don haka mu gane kamar yadda suka zama kanwa uwar gami wurin farraka Sudan-ta-Kudu ta hanyar amfani da bambanci kabila haka za su farraka Najeriya ko da an rabu. Don haka mu hada kanmu, mu samar da shugabanci nagari, ba wai kururuwar raba Najeriya ba. Idan kunne ya ji jiki ya tsira.
Dangane da Sudan-ta-Kudu kuwa komai a kasar ya zama sama-a-kasa, babu tsabtataccen ruwan sha ko wutar lantarki ko asibitoci, ga zaman zullumi da fargaba. Da al’ummar Sudan-ta-Kudu sun hada kai da Sudan, sun dinke barakar da ke tsakaninsu, sun kuma sanya kishin kasarsu, da hakan ba ta faru ba, amma sai suka buge da jin zugar Amurka da ‘yan kanzanginta, wanda a yanzu aka kai su aka baro, kodayake masu iya magana dai sun ce munafunci dodo ne, mai shi yakan ci.

Bashir ya rubuto daga karamar Hukumar Jama’are, Jihar Bauchi.
Za a iya samunsa a wannan lambar: 07036925654

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno