Sudan ta Kudu ta daga zaben shugaban kasa

Shugaban Sudan ta Kudu Salba Kiir ya ce ya dage zaben da ya shirya gudanar wa a kasar a shekara mai zuwa saboda ya kara ba bangarorin da ke rikici damar yin sulhu a tsakaninsu.Tsarin mulkin kasar da ake amfani da shi na wucin gadi, ya tsai da watan Juli badi ne don gudanar da […]

Sudan ta Kudu ta daga zaben shugaban kasa
Sudan ta Kudu ta daga zaben shugaban kasa

Shugaban Sudan ta Kudu Salba Kiir ya ce ya dage zaben da ya shirya gudanar wa a kasar a shekara mai zuwa saboda ya kara ba bangarorin da ke rikici damar yin sulhu a tsakaninsu.
Tsarin mulkin kasar da ake amfani da shi na wucin gadi, ya tsai da watan Juli badi ne don gudanar da zaben. Amma ranar Lahadin da ta gabata bayan saukarsa a filin jirgin saman garin Juba, Shugaba Kiir ya bayyana dage zaben zuwa shekara biyu zuwa uku ma su zuwa.
kasar dai ta fada yakin basasa ne cikin watan Disambar bara, biyu bayan zargin juyin mulkin da Mista Kiir yake wa mataimakinsa Riek Machar wanda da ma ya rigaya ya dakatar da shi a watan Juli bara. Dalili da yakin basasar, kasar ta kasa samun damar hakar mai fetur din da tattalin arzikin kasar ya dogara da shi.
A ranar Juma’ar da ta gabata ne dai shugaban kasar da mataimakinsa suka sanya hannu a wata yarjejeniyar zaman lafiya da kuma ta bkafa wata gwamnatin rikon kwarya wanda ake fatan za ta kawo karshen rikicin da aka kwashe watanni biyar ana yi. Amma da alama yarjejeniyar ba ta kai zuci ba, saboda an ci gaba samun rahotannin rikici. Inda dakarun gwamnati da kuma na ’yan tawaye suke zargin juna da ta da wa. Har-ila yau, a ranar Litinin da ta gabata ne ’yan tawayen suka bayyana cewa dakarun gwamnati sun karbe iko da garin Bentiu, wanda babban birnin jihar nan ce mai arzikin mai fetur, wato Jihar Unity.
Sai dai  kasashen duniya ciki har da Amurka ba su yi na’am da dage zaben ba. Mista Machar ya bayyana cewa Shugaba Kiir ya yi haka ne don ya kara tsawaita wa’adin mulkinsa.
kasar dai ba ta taba gudanar da zabe ba. A watan Janairun shekara 2011ne dai ’yan kasar suka zabi ballewa daga kasar Sudan. Bayan ballewarsu Mista Kiir ya zama shugaban kasa saboda shi ne babban jagora daga yankin na Sudan ta Kudu.