‘Sudan ta Kudu tana gab da fadawa cikin yakin basasa’

Shugaban Kwamitin Sulhu na Majalisar dinkin Duniya Mista Gerard Araud ya ce rikicin da ake yi a Sudan ta Kudu wanda ake ganin na kabilanci ne zai iya jefa kasar a cikin yakin basasa.Mista Araud ya gaya wa BBC cewa Majalisar dinkin Duniya ta samu rahotannin da ke nuna cewa an kashe daruruwan mutane tun […]

‘Sudan ta Kudu tana gab da fadawa cikin yakin basasa’

Shugaban Kwamitin Sulhu na Majalisar dinkin Duniya Mista Gerard Araud ya ce rikicin da ake yi a Sudan ta Kudu wanda ake ganin na kabilanci ne zai iya jefa kasar a cikin yakin basasa.
Mista Araud ya gaya wa BBC cewa Majalisar dinkin Duniya ta samu rahotannin da ke nuna cewa an kashe daruruwan mutane tun lokacin da aka yi yunkurin juyin mulki a kasar a ranar Lahadi, kodayake ya ce, fadan bai cika shafar farar hula ba.
Ya ce wasu mutanen kimanin dubu 20, sun nemi mafaka a ofishin Majalisar dinkin Duniya da ke Juba babban birnin kasar kuma magunguna da abincin da majalisar ke da su domin kula da dimbin mutanen na neman karewa.
Shugaban Sudan ta Kudu Salba Kiir ya dora laifin yunkurin juyin mulkin kan sojojin da ke biyayya ga tsohon mataimakinsa Riek Marchar wanda ba dan kabilarsu ba ne.
A ranar Litinin ne Shugaba Kiir ya ce kasar tana yunkurin murkushe yunkurin juyin mulkin da sojoji masu biyayya ga Mista Machar suke yi. Yunkurin ya zo ne bayan jin karar harbe-harbe cikin dare a babban birnin kasar Juba.
Mista Kiir ya fadi a wani taron manema labarai cewa gwamnati tana ci gaba da iko da babban birnin kasar kuma ya kafa dokar hana yawon dare ga fararen hula.
Wakiliya ta musamman ta Majalisar dinkin Duniya a kasar Misis Hilde Johnson, ta bukaci “dukkan bangarorin da ke fadan su hanzarta mayar da wukakensu.”
Mista Riek bai ce uffan ba, kuma ba a san inda yake ba, amma kakakinsa ya ce yana nan lafiya kuma ya musanta rahotannin cewa an kama shi.
Zaman dar-dar ya karu a Sudan ta Kudu – kasa ta baya-bayan da ta samu ’yanci a duniya- tun lokacin da Shugaba Kiir ya rushe Majalisar Zartarwarsa ciki har da Mista Machar a watan Yuli.
Ana alakanta rushe majalisar da rigimar neman iko – kuma an ce Mista Machar yana shirin fitowa takarar Shugaban kasar a shekarar 2015. A yanzu yana jagorantar wani bangare a cikin Jam’iyyar SPLM.
Mutanen biyu sun fito ne daga kabilu biyu da suka yi fada da juna a baya, inda Mista Kiir ya fito daga kabilar Dinka mafi girma a kasar, yayin da Mista Machar ya fito daga kabilar Nuer ta biyu. Wasu ’yan kabilar Nuer na zargin ’yan kabilar Dinka da danniyar siyasa.