Sufeto Janar ya bayyana gaban ’yan majalisa amma ya ki amsa tambaya
Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Ibrahim Idris jiya ya bayyana gaban kwamitin bincike na majalisar dokoki kan zargin da Sanata Isah Hamma Misau ya yi masa amma kuma ya ce ba zai amsa kowace tambaya ba. Shugaban Kwamitin, Sanata Francis Alimkhena, dan jam’iyyar APC daga jihar Edo bayan ya gabatar da ’yan kwamitin ya tambayi […]
Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Ibrahim Idris jiya ya bayyana gaban kwamitin bincike na majalisar dokoki kan zargin da Sanata Isah Hamma Misau ya yi masa amma kuma ya ce ba zai amsa kowace tambaya ba.
Shugaban Kwamitin, Sanata Francis Alimkhena, dan jam’iyyar APC daga jihar Edo bayan ya gabatar da ’yan kwamitin ya tambayi Sufeto Janar din ya yi karin bayani kan zarge-zargen da ake yi masa.
Amma lauyan Sufeto Janar din, Alex A. Izinyon wanda ya zauna kusa da shi ya ce ina son na bayyana kasancewa ta gaban kwamitin, sai shugaban kwamitin ya tambayi lauyan “Shin kai ne Sufeto Janar”.
A wannan lokaci sai Sufeto Janar ya ce ba zan ce uffan ba ko na amsa wata tambaya dange da zarge-zargen da ake yi mini saboda shari’ar da ke gudana a kotu.