Sukurkucewar al’amuran al’umma: Sabubba da maganinsu (1)

Daga Sheikh Ali Abdur-Rahman Al-Huzaifi, Masallacin Annabi (SAW), Madina Huduba ta farkoDukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga Manzon Allah da alayensa da sahabbansa.Bayan haka, ya ku Musulmi! Ku ji tsoron Allah, ku yi riko da Musulunci, domin shi ne igiya amintatta. Kuma jin tsoron Allah […]

Sukurkucewar al’amuran al’umma: Sabubba da maganinsu (1)
Sukurkucewar al’amuran al’umma: Sabubba da maganinsu (1)

Daga Sheikh Ali Abdur-Rahman Al-Huzaifi, Masallacin Annabi (SAW), Madina

Huduba ta farko
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga Manzon Allah da alayensa da sahabbansa.
Bayan haka, ya ku Musulmi! Ku ji tsoron Allah, ku yi riko da Musulunci, domin shi ne igiya amintatta. Kuma jin tsoron Allah ne ke daidaita al’amuran rayuwar kowane mutum a nan duniya da kuma Lahira.
Ku sani, Sunnar Allah (hanyar da Ya tsara wa halittarSa), ba ta canjawa a wannan duniya. Allah Madaukaki Ya ce: “To ba za ka samu musanya ba ga Sunnar (hanyar) Allah. Kuma ba za ka samu juyarwa ba ga hanyar Allah.” (k:35:43).
Sunnar Allah ce cewa duk wanda ya shuka mai kyau, zai girbi mai kyau, kuma duk wanda ya shuka mummuna, zai girbi mummuna. Allah Ya ce: “Kuma wanda ya aikata (wani aiki) gwargwadon nauyin zarra na alheri, zai gan shi. Kuma wanda ya aikata gwargwadon nauyin zarra na sharri, zai gan shi.” (k:99:7-8).
Sunnar Allah ce a kan bayinSa cewa duk wanda ya zabi hanyar jin dadin rayuwar duniya da kawarta, zai samu abin da Allah Ya kaddara masa a nan duniya, kuma wanda ya zabi gidan Lahira da gidan Aljanna, Allah zai biya masa bukatarsa. Kuma duk wanda ya nemi dukkansu biyu, duniya da Lahira kuma ya bi Allah tare da kaurace wa aikata zunubai, zai samu dukkan biyun. Allah Ya ce: “Wanda ya kasance yana nufin mai gaggawa (duniya), sai Mu gaggauta masa a cikinta, abin da Muke so ga wanda Muke nufi, sannan kuma Mu sanya masa Jahannama, ya konu da ita, yana abin zargi kuma abin tunkudewa. Kuma wanda ya nufi Lahira kuma ya yi aiki saboda ita, irin aikinta, alhali yana mumini, to, wadannan aikinsu ya kasance godadde. Dukkansu Muna taimakon wadannan da wadancan daga kyautar Ubangijinka, kuma kyautar Ubangijinka ba ta kasance hananna ba.” (k:17:18-20).
Har wa yau yana cikin Sunnar Allah Ya jarrabi bayinSa da abu mai kyau da marar kyau. Allah Madaukaki Ya ce: “Kuma Muna jarraba ku da sharri da alheri a matsayin fitina. Kuma zuwa gare Mu ake mayar da ku.” (k:21:35)
 Shi Musulmi duk lokacin da ya samu alheri ya san rahama ce daga Allah, domin ya san ba ya da ikon da zai ce yana da wani hakki a kan Allah da zai sa Ya yi masa haka. Wannan irin imani zai sanya shi ya yi gdiya ga Allah Ya yi yabo gare Shi. Sannan idan wani sharri ya same shi, sai ya yi hakuri ya nemi lada a wurin Ubangijinsa, domin ya san imma hakan ya faru da shi ne saboda wani laifi da ya yi, ko kuma Allah Yana nufin Ya daukaka matsayinsa ne a Lahira. Allah Madaukaki Ya ce: “Kuma abin da ya same ku na wata masifa, to game da abin da hannayenku suka sana’anta ne, kuma Allah Yana yafewar (wadansu laifuffuka) masu yawa. (k:42:30).
Don haka wajibi ne Musulmi ya rika yi wa kansa hisabi ya rika aunawa da nazarin ayyukansa, ya rika tuba kan kowane laifi da ya aikata.
Shi kafiri duk lokacin da ya samu alheri, sai ya shiga alfahari da girman kai, ya fara zalunci. Kuma a duk lokacin da masifa ta same shi, sai ya yi ta kuka, ya kasa hakuri. Duniya ita ce Aljannarsa, son zuciyarsa shi ne abin bautarsa.
’Yan uwa a cikin imani! Musulmi a yau suna fama da bala’o’i. Kuma ana jingina wadannan bala’o’i kan wasu abubuwa:
Wadansu su ce miyagun shirye-shirye ne na makiya; wadansu su ce mummunan talaucin da ake fama da shi ne; wadansu kuma su ce saboda ci baya da Musulmi suke da shi ne a fannin ilimin kimiyya da masana’antu da sauran dalilai.
Wadannan dukkansu alamu ne na bayyanar cutar. Amma ainihin abin da ya jawo wannan mummunan hali shi ne Musulmi suna yi wa addininsu rikon sakainar kashi a daidaikunsu da kuma a hukumance. Allah Madaukaki Ya ce: “Shin kuma a lokacin da wata masifa, hakika ta same ku, alhali kuwa kun samar da biyunta kun ce: “Daga ina wannan yake?” Ka ce: “Daga wurin rayukanku yake.” Lallai ne Allah, a kan dukkan komai, Mai ikon yi ne.”  (k:3:165).
Kuma Ya sake cewa: “Lallai ne, Allah ba Ya canja abin da yake ga mutane, sai sun canja abin da yake a zukatansu.” (k:13:11).
Musulmi a tarihinsu, sun samu kansu a wasu lokuta da suka fi yanzu tsanani da wahala, inda makiyansu suka ci zarafinsu. Amma da suka koma ga addininsu, komawa bisa gaskiya da ilimi da imani, sai suka samu aminci, mutuncinsu ya dawo, hadin kai da jin dadi suka samu a tsakaninsu a karkashin inuwar shari’ar Musulunci. Sai suka samu waraka daga wannan cuta, halin da suke ciki ya kyautatu.
A wannan lokaci da muke ciki, babu shakka bala’o’in da suke fuskantar al’ummar Musulmi suna da yawa da kuma tsanani, amma abin da ko shakka babu shi ne, rayuwar Musulmin yau ba za ta koma daidai ba, har sun koma ga gwadaben magabatansu. Don haka dora wa makiya Musulunci alhakin wadannan bala’o’i, ba zai sa a wanke Musulmi daga gazawarsu da jawo wa kawunansu bala’o’i da ci baya ba. Domin yaushe ne Musulmi za su sa ran kafirai su warware musu matsalolinsu? Don me ba za su gyara da kansu ba ta hanyar komawa ga Littafin Allah da Sunnar ManzonSa (SAW), domin amfanin kansu da ’ya’yansu masu zuwa?
Don haka maganin matsalolin Musulmi yana hannun Allah ne, sannan kuma yana hannun shugabanninsu da malamansu ta hanyar yi musu umarni da dukkan alheri da karfafa musu gwiwar aikata alheri da hana su aikata abin ki, kamar yadda addininsu ya koyar. Wannan babban nauyi ne da ke bukatar karfin niyya da azama da gaskiya.

Za mu cigaba, insha Allah