Sulaiman Muhammed: Edita mai saukin kai ya kwanta dama

Allah sarki! Mutuwar Sulaiman Muhammed ta tabbatar da mafarkin da na yi mako guda kafin mutuwarsa, inda aka nuna mini cewa daya daga cikin editocin kamfanin Media Trust da yake aiki a hedikwatar kamfanin da ke daura da Otel din Chida na Abuja ya rasu. To amma ban gaya wa kowa ba sai da lamarin […]

Sulaiman Muhammed: Edita mai saukin kai ya kwanta dama
Sulaiman Muhammed: Edita mai saukin kai ya kwanta dama

Allah sarki! Mutuwar Sulaiman Muhammed ta tabbatar da mafarkin da na yi mako guda kafin mutuwarsa, inda aka nuna mini cewa daya daga cikin editocin kamfanin Media Trust da yake aiki a hedikwatar kamfanin da ke daura da Otel din Chida na Abuja ya rasu. To amma ban gaya wa kowa ba sai da lamarin ya auku.
Babu shakka lokacin da na samu labarin mutuwarsa na dimauce saboda a nan Jihar Legas ba mu gama jimamin mutuwar daya daga cikin direbobinmu ba, mai suna Efosa wanda ya rasu sakamakon shanyewar barin jikinsa da kuma bugun jinin da ya samu a zuciyarsa.
Ban gushe ba ina tuna lokacin da na hudu da shi a kamfanin Media Trust shekaru 10 da suka wuce, a lokacin ya na matsayin Editan Siyasa na jaridar Daily Trust, ni kuwa ina sabon ma’aikaci inda aka turani Jihar Gombe a matsayin wakili mai aiko da labarai. Saboda irin shawarwarin da yake ba ni kan yadda zan gyara rubutuna nake girmama shi. Kuma shi ne dan jarida na farko da na rika koyon yadda ake rubuta labarin siyasa ta hanyar rubutunsa da ake bugawa a jarida. Ya kasance duk rubutun da ya yi ba ya wuce ni sai na karanta shi, musamman ma idan ya yi sharhi a kan wani al’amarin siyasa.
Mun shaku da shi sosai lokacin da aka mayar da shi Editan labarai na jaridar Daily, inda ya rika ba ni shawarwari masu amfani da suka rika taimaka mini a aikina na jarida. Daga baya da aka dawo da ni ofishin mu na Abuja da ke kan titin Lusaka sai na mayar da shi tamkar yayana saboda irin kaunar da yake nuna mini. Wani abu da ba zan taba mantawa da shi ba, shi ne na taba kai masa karar wani abokin aikina cewa ya zalunce ni, sai ya ce mini na yi hakuri kuma kada na ce zan rama abin da ya yi mini.
A lokacin da na samu aiki da  sashen Hausa na rediyon Duche Welle na kasar Jamus, Sulaiman shi ne ya yi sanadin na sauya ra’ayina na ci gaba da aiki da kamfanin Media Trust, domin lokacin da na nemi shawararsa sai ya ce da ni Abubakar ka yi tunani kai sabon dan jarida ne yanzu ka fara aikin jarida kamata ya yi ka tsaya ka koyi aikin sosai kafin ka ce za ka koma bangaren rediyo. Ya ce mini mai ka rasa a Media Trust, sun dauke ka cikakken ma’aikaci, suna biyanka albashi a kan kari da sauran alawus-alawus. Su kuwa can da za ka je za su dauke ka ne a matsayin ma’aikacin wucin-gadi daga karshe idan shekarunka sun kare sai su sallame ka. Amma daga karshe sai ya ce na je na yi tunani kafin na yanke shawara. Daga karshe na rika addu’ar Allah ya zabar mini mafi alheri. Na ci gaba da aiki a Kamfanin Media Trust.
A lokacin da zan koma Aminiya ma sai da na shawarce shi amma sai ya tambaye ni dalili, da na gaya masa sai ya ce na je na yi addu’a kafin na koma. Wani abu da na koya a wurinsa shi ne hakuri da zama da mutane lafiya, don ban taba jin wanda ya yi korafi a kansa ba. Ko a Jihar Legas ma’aikata da ma sun yi ta bayyana irin hakurinsa da kuma yadda ya iya zama da mutane.
Wata rana na je wurinsa zan yi bankwana da shi cewa zan tafi Legas, farkon abin da ya fara gaya mini shi ne na yi gaskiya kuma na rike amanar da aka dora mini. Sannan ya gaya mini sirrin aiki a Jihar Legas wanda ya amfane ni sosai. Kodayaushe muka yi waya sai ya rika tsokana ta yana cewa na zama dan  Legas.Wata dabi’a da na koya daga gare shi ita ce daukar rayuwa da sauki. Sulaiman bai dauki rayuwa wani abu ba, kuma ba ya tayar da hankalin sa a kan wani abu.
Shawarwarin da ya rika ba ni sun yi min amfani a rayuwata da kuma harkar aikina wannan ne ya sa ba zan taba mantawa da shi ba har abada. Allah ya jikansa ya gafarta masa ya kuma amfani zuriyarsa. Matarsa da iyayensa da ’yan’uwansa Allah ya ba su hakurin jure rashin da suka yi.

Abubakar Haruna, 08027406827