Suleiman: Maginin da yake amfani da bulon tavo da ya fi na siminti inganci
Suleiman Hamza dan asalin Jihar Katsina da ke sana’ar gini a kauyen Kuchibuyi a karamar Hukumar Bwari da ke Abuja, ya bayyana yadda ya fara sana’ar gini, nasarorin da ya samu da kuma matsalolin da yake fuskanta: Aminiya: Yaya ka fara sana’ar gini?Suleiman: Na fara sana’ar gini tun ina Katsina shekara biyar da ta gabata. […]
Suleiman Hamza dan asalin Jihar Katsina da ke sana’ar gini a kauyen Kuchibuyi a karamar Hukumar Bwari da ke Abuja, ya bayyana yadda ya fara sana’ar gini, nasarorin da ya samu da kuma matsalolin da yake fuskanta:
Aminiya: Yaya ka fara sana’ar gini?
Suleiman: Na fara sana’ar gini tun ina Katsina shekara biyar da ta gabata. Na bar Katsina ne saboda muna da yawa wadanda suke aikin gini. A nan Abuja babu masu aikin gini masu yawa, hakan ya sanya nakan samu alheri sosai. Na zo nan Abuja shekara 5 da ta gabata, amma ina jin dadin yadda aikina yake tafiya. Wani maigidana ne ya koya mini aikin gini a Katsina, na kuma zo nan ne ta hanyar ’yan uwana da suke zaune a nan.
Aminiya: Da yaya kake samun aiki a wurin mutane?
Suleiman: Jama’a da yawa sun san ni, saboda ina yi musu aiki mai kyawu. Haka za ka ga mutane sun same ni don in ba su shawarar yadda gininsu zai kasance. Ya danganta da irin ginin da mutum yake so ne. Wani lokaci wanda za a yi masa gini yakan samar da tavo sai in yi masa bulo, idan ya bushe, sai in yi masa ginin da shi. Ba na amfani da siminti, da tavo nake amfani, bulo dina ya fi na siminti karfi. Idan na kammala ginin, sai mutum ya zavi irin kasar da yake so a yi masa yave.
Aminiya: Kamar a nawa kake yi wa mutane gini?
Suleiman: Nakan gina ciki da falo a kan Naira dubu 20, wannan idan wanda za a yi wa ginin zai kawo tavo ke nan, aikina in yi masa bulo sannan in yi masa gini mai inganci. Yakan dauke ni wata daya in yi bulo, in kuma gina gida, saboda yaro daya nake da shi.
Aminiya: Bayan gini ko kana wani aikin?
Suleiman: A nan Abuja aikin gini kawai nake yi, amma idan lokacin damina ne nakan koma Katsina in yi noma, bayan an yi girbi sai in komo Abuja, haka nake duk shekara.
Aminiya: Wadanne kalubale ka fuskanta?
Suleiman: A gaskiya a nan mutane ba su cika ginin gida ba, saboda babu kudi a wurin mutane. Idan na yi aiki yau ban san wane lokaci za a sake kirana ba. Wani lokaci kuma sai ka kammala aiki, amma batun biyan kudi ya zama tashin hankali, inda za su rika sanya ka jeka ka dawo. Wadansu kuma neman araha.