Suleiman Yahaya ya zama shugaban kamfanin siminti na Ashaka
Malam Yahaya Suleiman ya zama sabon shugaban kamfanin siminti na Ashaka. Kamfanin Ashakacem kamar yadda aka yi masa rijista a Kasuwar Hannun Jari ta Najeriya wani rukuni ne kamfanin Lafarge SA da ke samar da siminti, inda bayan wa’adin Alhaji Umaru kwairanga ya kare ne Yahaya ya zama sabon shugaban kamfanin. Sabon shugaban kamfanin ya […]
Malam Yahaya Suleiman ya zama sabon shugaban kamfanin siminti na Ashaka.
Kamfanin Ashakacem kamar yadda aka yi masa rijista a Kasuwar Hannun Jari ta Najeriya wani rukuni ne kamfanin Lafarge SA da ke samar da siminti, inda bayan wa’adin Alhaji Umaru kwairanga ya kare ne Yahaya ya zama sabon shugaban kamfanin.
Sabon shugaban kamfanin ya fita da shaidar digiri mai daraja ta daya a kan kwas din tsimi da tanadi a Jami’ar Cambridge, inda ya samu kwarewa a kan harkokin gudanarwa. Kafin ya zama sabon shugaban kamfanin ya kasance daya daga manyan jami’an gudanarwar kamfanin.
Shi ne shugaban kamfanin NAHCo, sannan shugaban gudanarwa na kamfanin Rosehill Group, shi ne ya kirkiro Asokoro Island da ke Abuja.
Sabon shugaban yana da shekara 51, an kuma karrama shi da lambar girmammawa ta OON.