Suleman Hashimu ya zama abun koyi
Suleman Hashimu matashin da ya dabo sayyada daga Ikko zuwa Abuja,ya nuna wa matasan Najeriya yadda ake amfani da basira wajen fita daga sahun ya ku bayi.Koda bai samu komai ba,to ya ajiye tarihi wanda za a dade ba a manta da shi ba.Maimakon shaye-shayen miyagun kwayoyi da matasa suka mayar da hankali a kai,ko […]
Suleman Hashimu matashin da ya dabo sayyada daga Ikko zuwa Abuja,ya nuna wa matasan Najeriya yadda ake amfani da basira wajen fita daga sahun ya ku bayi.Koda bai samu komai ba,to ya ajiye tarihi wanda za a dade ba a manta da shi ba.Maimakon shaye-shayen miyagun kwayoyi da matasa suka mayar da hankali a kai,ko kallon kwallo da fina-finan batsa,kamata ya yi matasan Najeriya su yi koyi da Suleman Hashimu. A nan ba dole sai mutum ya yi tafiyar kasa ba,a’a ai duk dan Adam,Allah ya hore masa baiwa.Baiwar Suleman Hashimu a tafiyar kasa take.Ya yi tafiya daga Legas zuwa Abuja ba tare da ya yi koda tuntube ba,kuma bai yi koda rashin lafiya ba.Masu iya magana na cewa idan wani ya yi rawa ya samu kudi,wani idan ya yi,kashi zai sha.Yanzu haka wani ko miliyan dari za a saka masa,ba zai iya tafiya daga Legas zuwa Abuja a kasa ba.Wani in ya kwatanta to sai dai a dauko gawarsa,saboda ba nan baiwarsa take ba.Saboda haka, a matsayinka na matashi,sai ka tsaya,ka tambayi kanka da kanka,cewa ni kuma me zan kirkiro wanda duniya za ta yi marhabin da shi? Me zan yi wanda wani mahaluki bai taba yi ba? Ba dole don neman suna ko daukaka ba.Ka yi abin da idan kana yin sa,za ka ji kana son sa.Misali,koda aikinka yankar farce ne,to me zai hana ba za ka fito da wani sabon salo a sana’ar wanda zai sa a san ka ko ina a duniya? Akwai mutane da yawa a duniya da aka rubuta sunansu a kundin tarihi,saboda sun yi tunani mai zurfi,kuma sun jajirce don aiwatar da tunanin.Kai me zai hana ka yi irin wannan?
Ka daina tunanin matsalar abu,a kullum ka duba mafita.Duk mutumin da a kullum matsala yake fara dubawa ba mafita ba,to bai cika tabuka wata tsiya a rayuwa ba.Da Suleman Hashimu,ya dubi hadarin da yake tattaren da bin hanyar Legas a kasa,wanda ya hada da gamuwa da ‘yan fashi ko matsafa,ko makiya su yi amfani da wannan damar su halaka shi,ko makiyan Baba Buhari su huce haushi a kansa,to da bai yi wannan tafiyar da ya yi ba,kuma da ya rasa wata gagarumar dama a rayuwarsa ciki har da haduwa da Sarakunan Bidda da Minnna da Agei da Suleja da Zuba.Da bai yi ido hudu da Baba Buhari ba,kazalika da bai hadu da mutane daban-daban da ya hadu da su ba;da bai yi sunan da ya yi ba.Duk ya samu haka ne saboda yana da tunani mai kyau,wanda ya saba da tunanin mutane gama-gari da a kullum suke kallon matsala maimakon mafita.
‘Yan Najeriya kamata ya yi mu yi koyi da rayuwar Suleman,maimakon yi ma sa hassada,da zargin cewa akwai lauje a cikin nadi.Wasu na tunanin ba zai yiwu mutum ya yi tattaki daga Ikko zuwa Abuja cikin kwanaki 18 ba.Masu irin wannan tunanin ba kasafai suke iya tabuka abin al’ajabi a rayuwarsu ba.Ba su iya komai sai gulma,sai kage da sharri,haka za su gama rayuwarsu ba tare da kowa ya san su ba.Mallam tashi daga zaman tsurku,ka kirkiri abin da zai jefa sunanka,a kundin mutane fitattu shahararru.Kai mai fadin karya ce,bai yiwuwa mutum ya taho a kasa tun daga Legas zuwa Abuja,me ya hana ka kirkiro koda irin wanan karyar ce?In ma karya ce,to lalle karyar tana da amfani,domin a yanzu haka ta tunzura wasu su ma sun bi sahu,kamar yadda wani ya dabo sayyada daga Yola zuwa Abuja,da kuma yadda wani ya taho a kasa daga Abuja zuwa Makurdi don shaida rantsuwar sabon Gwamnan jihar Benue.
A kasashen da aka ci gaba,da a lokacin da Suleman ya kudiri aniyarsa ta yin takakkiya daga Legas zuwa Abuja,to da gwamnati da kanta za ta tura tawaga guda su raka shi,cikin tawagar za a samu jami’an kiwon lafiya da jami’an tsaro wadanda za su ba shi kariya,don su tabbatar miyagu ba su cutar da shi ba.To amma da yake a Najeriya ne,shi kadai ya taho koda kuwa kuraye za su cinye shi.
Kiran da zan yi wa gwamnati shi ne,duk wanda zai yi irin wannan tafiya mai hadari,to ya kamata a ba shi kariya,tun daga inda ya fara tafiyar har inda zai isa.Shi kuma Suleman muna fatan kamfanoni masu zaman kansu za su fara daukar sa aiki don ya rika tallata masu hajarsu,musamman kamfanonin abin tsotse-tsotse da lashe-lashe kamar 7Up,Cocala da sauransu.Kazalika,ya kamata gwamnatin Janar Buhari ta karrama duk wanda ya yi irin wannan bajinta.A ba su gurabun karo karatu idan suna so,a kuma ba su aiki mai tsoka.
Kwamared Bishir Dauda Sabuwar Unguwa katsina, Babban Sakataren kungiyar Muryar Talaka ta kasa
08165270879