“Sulhu ba zai yiwu a karkashin dokar ta-baci ba”

Shugaban kungiyar Kare Hakkin dan Adam ta Cibil Right Congress of Nigeria (CRC), Shehu Sani ya bayyana cewa dokar ta baci da Gwamnatin Tarayya ta kafa wa jihohin Yobe da Borno da Adamawa ba wani abu ba ne face kama-karya, saboda abu ne mai wahala a yi sulhu a karkashin dokar ta-baci, kuma hakan zai […]

“Sulhu ba zai yiwu a karkashin dokar ta-baci ba”
“Sulhu ba zai yiwu a karkashin dokar ta-baci ba”

Shugaban kungiyar Kare Hakkin dan Adam ta Cibil Right Congress of Nigeria (CRC), Shehu Sani ya bayyana cewa dokar ta baci da Gwamnatin Tarayya ta kafa wa jihohin Yobe da Borno da Adamawa ba wani abu ba ne face kama-karya, saboda abu ne mai wahala a yi sulhu a karkashin dokar ta-baci, kuma hakan zai sa masu kai hare-hare su ci gaba da abubuwan da suke yi.
Malam Shehu Sani ya bayyana haka ne a wata tattaunawa, inda ya ce dokar ta-bacin da aka ayyana ba wani abu ba ne, face an fake da guzuma an harbi karsana wajen tauye hakkin dan Adam da kuma bayar da damar a aikata duk wani cin zarafi.  
Ya ce, katse wayoyin sadarwa a shiyyar Arewa maso Gabas wata azabtarwa ce ga daukacin mutanen wannan yanki, kuma a fili yake an tauye musu hakkinsu na sadarwa da mu’amala da kai-kawo a tsakanin junansu.
“Ba zai yiwu mu ci gaba da tauye hakkin dan Adam da sunan tsaro ba. Wajibi ne dimokuradiyya ta samar da dabaru da hanyoyin magance dukkan hare-hare ta hanyoyin da suka dace da ita. Amma abin da ke faruwa a jihohin Borno da Yobe da Adamawa babban laifi ne, kuma kazanta ce ga dimokuradiyyarmu da hakan ke zubar da mutuncin gwamnatin Shugaba Goodluck Jonathan. ’Yan Najeriya sun gaji da labaran kanzon kurege da hukumomin tsaro ke ba su ba tare da gano gaskiyarsu ba. Kuma ina yaba wa gidan talabijin na Aljazeera kan rahotannin gaskiya da yake bayarwa game da cin zarafin dan Adam da jami’an tsaro suke yi ga jama’ar da ba su san hawa ba, bare sauka a wadancan jihohi,” inji shi.
Ya ce katse hanyoyin sadarwa ya kawo nakasu ga harkokin kasuwanci da ilimi da rayuwar jama’ar jihohin da dokar ta shafa, kuma ya raba su da abokan arziki da suke sauran sassan kasar nana da sauran kasashen duniya. “Wannan wata gamammiyar azaba kusan ga daukacin ’yan Najeriya da suke zaune a wannan yanki na kasar nan. Katse hanyoyin sadarwa ba zai kawo karshen hare-hare ba, kuma ta kowace fuska ba zai hana mahara yin abubuwan da suke yi ba; maimakon haka zai kara kawo kunci ne ga ’yan Najeriyar da lamarin ya rutsa da su,” inji shi.
Ya kara da cewa, “Idan gwamnati da hukumomin tsaro suna da yakini kana bin da suke yi cewa gaskiya ne kuma ya dace, to babu dalilin da za su tauye hakkokin wasu jama’a, kamar manema labarai da daidaikun jama’a daga gudanar da harkokinsu. Ko a lokacin yaki; akan bar ’yan jarida su gudanar da ayyukansu; don haka a ganina, dokar ta-bacin abar Allah wadai ce, kuma a matsayinmu na kungiyar kare hakkin dan Adam za mu kalubalanci katse wayoyin sadarwa da dokar ta-bacin da tauye hakkin jama’a da ake yi ta fakewa da dokar ta-bacin a kotu.”