Sulhu da Boko Haram: Wasu na murna wasu na shakka
A makon jiya ne Babban Hafsan Tsaro Iya Cif Marshal Aled Badeh ya bada sanarwar cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a tsakanin ’yan kungiyar Boko Haram da Gwamnatin Tarayya a karkashin kulawar shugaban kasar Chadi Mista Idris Debby, sai dai jama’a da dama a jihohin Yobe da Borno da suka fara fadin albarkacin bakinsu, wasu na […]

A makon jiya ne Babban Hafsan Tsaro Iya Cif Marshal Aled Badeh ya bada sanarwar cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a tsakanin ’yan kungiyar Boko Haram da Gwamnatin Tarayya a karkashin kulawar shugaban kasar Chadi Mista Idris Debby, sai dai jama’a da dama a jihohin Yobe da Borno da suka fara fadin albarkacin bakinsu, wasu na murna da fatan alheri ne, yayin da wasu ke nuna shakka da taraddadi.
Rahotanni sun ce wani mai suna danladi Ahmadu ne ya yi magana da yawun kungiyar kan amincewa da yarjejeniyar tare da alkawarin sako ’yan matan Chibok.
Sai dai daya daga cikin wadanda suka fara shiga tsakanin gwamnati da kungiyar Boko Haram, Sheikh Abubakar Diyar ya shaida wa Wakilinmu a Damaturu cewa akwai rikitarwa a cikin shirin sulhun da ake cewa ana yi tsakanin Gwamnatin Tarayya da ’yan kungiyar Boko Haram a yanzu.
Sheikh Abubakar Diyar wanda shi ne jagoran Salafiyawa da ke garin Damaturu, ya ce, yana ganin akwai matukar rikitarwa dangane da hakan domin kuwa a cewarsa da jagoran kungiyar Boko Haram din ne ya fito da kansa ya ayyana wannan batu to da an san da gaske lamarin yake.
Sheikh Diyar ya ce wannan kungiya ta Boko Haram kungiya ce da a yanzu ba ta da takamamme ko tsayayyen shugabanci a tare da ita, don haka da wuya a ce za a samu tsayayyar manufa da za a dogara da ita kan duk wata magana da aka yi.
Sheikh Diyar ya ce “A baya akwai wata kungiya da ake kira Ansaru da ta fito ta ce za ta iya shiga tsakani don sasanta wannan rikita-rikita amma kuma ai kin amincewa da ita muka yi saboda tunanin rashin tsayayyiyar manufa kan wannan kudiri nata.”
Ya ce a baya can an kafa kwamitocin sasanta wannan rikici da duniya ta san da su, na baya bayan nan su ne kwamitocin Minista Kabiru Turaki da wanda Gwamnan Borno Shettima ya kafa duk ba su yi komai ba sai a ce wannan kwamiti ya cimma matsaya da su, don haka a ganinsa akwai lauje cikin nadi kan wannan sanarwa.
Malam Usman dan Kanuri wani dan gudun hijira daga Konduga a Jihar Borno da ke Damaturu cewa ya yi lokacin da ya ji sanarwar tsagaita wutar ya ji dadi, domin wannan rikici ne ya yi sanadin raba su da garuruwansu suka shiga halin kuncin rayuwa a yanzu, don haka a cewarsa Allah Ya sa wannan batu da gaske ne ko sa samu komawa garuruwansu na asali.
Wani dan gudun hijirar daga Gujba da ke Damaturu da ya nemi a sakaye sunansa ya bayyana wa Aminiya cewa wannan sanarwa da farko ta faranta masa rai, to amma daga baya sai ya yi tunanin cewa an dade ana fadar irin hakan kuma sai a tarar lamarin ba haka yake ba. Malamin ya kara da cewa in har an cimma yarjejeniyar dakatar da bude wuta, me ya sa kwana daya da kulla yarjejeniyar a rika kai hare-hare a wasu garuruwan Jihar Borno har da kashe sama da mutum 40 da kone musu gidaje har ma an kame garin Abadam? Sai dai kuma shi sakataren Boko Haram din, watau dalladi Yakubu ya bayyana wa Muryar Amurka cewa ba ‘yan Boko Haram na ainihi ne suka ci gaba da kai harin ba.
Shi kuwa Malam Abdulrazak Ya’u mazaunin Damaturu, cewa ya yi kamata ya yi in har an samu lamari irin haka to a yi kyakkyawan zato ga wadanda suka ce suna kokarin kulla yarjejeniyar tare da addu’ar Allah Ya sa hakan ta tabbata, ba a sa tantama ciki ba.
Shi kuwa Malam Bukar Mala, wani dan kasuwa a Maiduguri, ya shaida wa Aminiya cewa “A gaskiya na yi murna da farin cikin jin wannan labari, ina fata Allah Ya tabbatar da sulhun kuma Ya sa da gaske ne. Ni dan kasuwa ne yau shekara 5 ke nan na samu karayar arziki, idan aka ce mun samu zaman lafiya zan iya sa ran zan farfado. Hanyoyin kan iyakokin Jihar Borno da kasashen Nijar da Kamaru da Chadi duk an toshe su ba a shigo da kaya ko fita da su, harkokin kasuwanci sun tsaya cik, don haka ina rokon Allah ya tabbatar da wannan sulhun da ake magana.”
Malam Gana daga Bama da ke zaman gudun hijira na Sansanin Masu Hidimar kasa a Maiduguri, ya ce “Ina rokon Allah Ya tabbatar da yarjejeniyar tsagaita wutar, domin mu samu mu koma garuruwanmu da aka kore mu, na rasa ’ya’ya 3 a harin Bama, kuma yakin Boko Haram ya durkusar da mu, muna zaune cikin wahala, ba wurin kwana mai kyau, ba abinci, ga sauro ga sanyi, don haka na ji dadin batun sulhun nan.”Ita kuwa Uwargida Marry James cewa ta yi “Muna rokon su sako mana ’yan matan Chibok duka, tare da fatan ba za su sake kashe kowa ba, muna son sulhu domin abin ya dame mu mun rasa inda za mu sa kanmu, abin ba kyau kuma ba dadi, Allah Ya kawo karshen wannan lamarin domin yara da mu mata muna shan wahalar rayuwa, an kashe mazajenmu an mayar da yara marayu, matakuma gwagware, a karshe sai ka ga mun koma muna bara, tunda ba wanda zai iya daukar nauyinmu da ’ya’yanmu.”
Sai dai Malam Muhammad Kachallah, ya ce “A gaskiya ban yarda da batun sulhun ba, inda gaskiya ne ai da Abubakar Shekau ne zai fito ya yi bayani cewa akwai wannan magana, domin an sha yin ruwa kasa na shanyewa. An sha yin irin wannan magana daga baya sai mu ji Shekau ya warware, don haka hukumomin Najeriya su je su daidaita da Boko Haram kafin su fada wa duniya halin da ake ciki. Kuma ai tun farkon maganar sulhu da aka shirya za a yi da mai shiga tsakani Dokta Datti Ahmed, an zargi bangaren gwamnati cewa ba da gaske take yi ba. Kuma su kansu Boko Haram din ana da tabbacin za su iya aje makamansu su shigo cikin mutane su iya gudanar da rayuwarsu kamar kowa? Wannan duk wani abin da mutane ya kamata su yi tunani a kai ke nan, saboda haka ni ban yarda ba, har sai na ga abin da ya faru.”
Shi kuwa Malam Sani Ibrahim mazaunin garin Maiduguri, cewa ya yi “A gaskiya ban yarda da batun tsagaita wuta da ake cewa za a yi da ’yan Boko Haram ba. Dalilina shi ne ’yan Boko Haram ba su da amana, ba sa girmama mutuncin mutum, kuma ba abin a yarda da su ba ne, ba su da alkawari kuma ba za su taba yarda su ajiye makamansu su shigo cikin mutane su rika gudanar da rayuwarsu kamar yadda kowa yake ba. Bayan sun dandani dadin kashe mutane, kana ganin za su iya bari, su shigo cikin mutane su ci gaba da rayuwa? Wannan wani abu ne da ya kamata jama’a da gwamnati su yi la’akari da shi, kuma ga shi ana maganar tsagaita wuta amma har yanzu suna kashe mutane a garuruwan Borno, ka ga wannan cin amana ne da karya alkawari. Ita ma gwamnati da nata laifin na daure wa Boko Haram gindi tare da yin kunnen uwar shegu da irin ayyukan ta’addancin da suke yi, kuma ai an zargi gwamnati da jan kafa a batun sulhun a baya, to ka ga abin ba zai yiwu da garaje ba. Sannan ya kamata a ce Shekau ne aka tattauna da shi ya bayar da sanarwar, saboda haka su yi a hankali kada ’yan ta’adda su yaudare su, su kuma su ci gaba da kashe mutane.”
Shi kuma Malam Modu Mala cewa ya yi “Mun dogara da Allah Shi ne kawai zai kawo mana karshen wannan bala’i, amma duk wani sulhu da Boko Haram ba zai yiwu ba sun riga sun cuce mu, sannan muna bukatar su sako mana ’yan matan Chibok, su daina kashe mu, in har suna so a yi sulhu kafin mu yarda da su, domin ba su da amana da alkawari. Ita ma gwamnati muna zargin ba ta son wannan abin ya kare, saboda haka muna rokon Allah Ya kawo mana karshen wannan bala’i da ya auka mana.”
Sai dai a yayin da wasu ke nuna shakka kan sulhun kasar Amurka ta ce bisa dukkan alamu an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a tsakanin gwamnatin Najeriya da mayakan Boko Haram din.
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka, Marie Harf ta ce a yanzu haka ana ci gaba da tattaunawa domin sako ’yan mata dalibai fiye da 200 da ’yan Boko Haram suka sace daga garin Chibok.
Gwamnatin Amurka ta aiko da kwararrun jami’an leken asiri da jirage marasa matuka domin taimaka wa jami’an tsaron kasar nan.