Sulhun Gwamna da ’yan majalisar Jihar Zamfara

Siyasar Jihar Zamfara ta dauki sabon salo, inda aka kai gwauro, aka kai mari, har al’amura da dama suka abku. A kan dambarwar yunkurin ‘yan majalisar Jihar Zamfara na tsige gwamnan jihar, wanda hakan ya haifar da abubuwa da dama, da ma sauye-sauye da alkawurra  da dama sun wakana. Manyan mutanen jihar da dama sun […]

Sulhun Gwamna da ’yan majalisar Jihar Zamfara
Sulhun Gwamna da ’yan majalisar Jihar Zamfara

Siyasar Jihar Zamfara ta dauki sabon salo, inda aka kai gwauro, aka kai mari, har al’amura da dama suka abku. A kan dambarwar yunkurin ‘yan majalisar Jihar Zamfara na tsige gwamnan jihar, wanda hakan ya haifar da abubuwa da dama, da ma sauye-sauye da alkawurra  da dama sun wakana. Manyan mutanen jihar da dama sun shigo don ganin an sulhunta. Domin a na su hangen wannan dambarwa a Jiharmu Zamfara babban koma baya ne. Sai dai fa kusan in ce; sulhun, da dama daga cikin talakawan jiha ba shi aka so ba.
Bisa la’akari da yadda cikin mako biyu da aka yi ana wannan balahirar, hakkokin talakawa da dama sun zo gunsu, haka abin da nike da tabbaci a nan shi ne, da ‘yan majalisar Jihar Zamfara ba su tauna tsakkuwa ba, da ba zai yi su ba. Kasancewar ma’aikatan jihar kwata-kwata sun manta da a a yi musu albashi a talatin ga wata, amma sanadiyar wannan balahirar, an biya albashi ma’aikatan Jihar Zamfara, tun a ranar 27 zuwa 28 ga.
Haka sama da Shekaru uku ke nan Gwamnatin Jihar Zamfara ba ta bai wa dalibban jihar tallafin karatu (Scholarship) ba. Amma da fara wannan balahirar, gwamnan da kansa ya kira kungiyar dalibbai ta Jihar Zamfara (NUZAMSS), tare da alkawarta biyan tallafin karatu (scholarship) nan take. Kuma kafin wannan lokacin ba irin binsa da ba mu yi ba, na ya tallafa wa rayuwar daliban ba, amma ko a jikinsa.
Haka ya kira matasa masu mu’amula da kafofin yanar-gizo (Social Media)  ya yi zaman da ko a da mafarki aka nuna wa wadannan matasa sun yi zama da gwamna sai sun karyata mafarkin kasancewar ya dauke su marasa amfani, duk da cewa suna tallata shi da jam’iyarsa. Sannan a wannan zaman ya yi musu goma ta arziki, tare da alkawarin tallafa musu ta kowane fanni. Da dai sauran abubuwan da gwamnan ya yi don dai ya samu yardar al’umma, da goyon bayansu. Wannan ke nan.
A ranar 30/7/2016 ne aka sasanta tsakanin gwamnan da ‘yan majalissar. To abin tambaya, wanda mu talakawan Jihar Zamfara muke son sani, shin wane alkawarin ne kuma gwamnan gwamnonin Najeriyar ya daukar muku da ma talakawan Jihar Zamfara, har ya sa kuka maar da wukar??
Kun fadi da dama daga cikin abubuwan da ya sa kuka yi yunkurin tsige shi. daya daga cikinsu, shi ne, yawan yawace-yawace, wanda tun kafin a shirya, ya shauda wa duniya cewa; ba wai dole ba ne sai yana cikin Jihar Zamfara ko Najeriyar ne zai iya mulki ba. A’a duk inda ya ke a duniya, zai iya mulkin Jihar Zamfara.
Mu talakawan Jihar Zamfara mun tabbatar da cewa yawace-yawacen gwamnan na daya daga cikin dalilan da ke hana shi kula da lamuranmu, kasancewar ko ba komai, ba don mu yake yin yawace-yawacen ba, sai don biyan bukatun kansa.
Don haka mu talakawan Jihar Zamfara za mu sanya ido mu ga   irin matsayar da kuka cinma har ya kai ga kun sauko, kasancewar tun da aka fara wannan danbarwar  talakawan jihar da dama muna ganin cewa ba don tauye rayuwar talaka da kasa sauke nauyin da ke kansa ba ne, sanadiyar wannan balahirar tsakaninku da gwamnan ba. A’a, sai don wasu abubuwa ne da kuka nema, ya ki biya muku, da kuma kin yarda ku zauna da shi duk lokacin da kuka bukaci hakan.
Ko dai mene ne lokaci zai nuna.  Canjin da kunka nema ya Tabbata. Dan haka yanzu sakonmu na farko ga gwamnan shi ne. Ya taimaki talakawan da ya karbe wa filaye da gidaje a unguwar Barakallahu da ke Gusau ko dai ya biya su diya ko kuma ya sakar musu filayensu. Tunda Shekaru uku ke nan bai yi yunkurin yin wani abu da su ba. Kuma bai biya su kudin diyar ba. Sannan mutun dubu da dari hudu da ya dauka aiki shekaru biyu, bai biya su hakkokinsu ba, muna jiran mu ji matakin da za ku dauka….
A karshe muna rokon Allah ta’ala ya ci gaba da kawo mana ci gaba mai dorewa a Jihar Zamfara da Najeriya baki daya.
Mai Biredi ya rubuto makalarsa daga tashar Bagu Gusau, shi ne Jami’in hulda da jama’a na kungiyar Muryar Talaka Ta kasa reshen Jihar Zamfara) 08069807496.