Sun auro wa mijinsu budurwa don su faranta masa rai

Uwargida da kishiya sun bai wa maigidan su mamaki a birnin Taif na kasar Saudiya, inda suka auro masa mata ta uku, wadda kuma ta fi su yarinta. Bhaya ga shawarar yin auren da suka bai wa mijin su, sun kuma ba shi taimako wajen gudasnar da shirye-shiryen bikin auren.Tsohon ango dan shekara 70, mai […]

Sun auro wa mijinsu budurwa don su faranta masa rai
Sun auro wa mijinsu budurwa don su faranta masa rai

Uwargida da kishiya sun bai wa maigidan su mamaki a birnin Taif na kasar Saudiya, inda suka auro masa mata ta uku, wadda kuma ta fi su yarinta. Bhaya ga shawarar yin auren da suka bai wa mijin su, sun kuma ba shi taimako wajen gudasnar da shirye-shiryen bikin auren.
Tsohon ango dan shekara 70, mai suna Awad bin Aouaimer Al-Thouaibi ya bayyana wa kafafen yada labaran kasar cewa, har ya dauka mafarki yake yi, ganin abin da matan sa suka yi masa. “Da farko na dauka suna son jin matsayina ne game da al’amarin. Sai kawai na fahimci daga gaske suke yi; suka kuma cewa, sun yi hakan ne don girmamawa da soyayya a gare ni. Don haka suke sanya ni farin ciki.
An gudanar da bikin auren a wani dakin taro da ke birnin na Taif, karkashin kulawar wadannan mata biyu, wato uwargida da kishiya. Ango Al-Thouaibi, wanda ke cike da farin ciki, ya yi ta yabon matansa, musamman ganin yadda suka cika alkawari har zuwa shirye-shirye ranar karshe ta bikin.
Ango da amarya sun tafi yawon shakatawa bayan kammala bikin auren su. “Ba zan taba mantawa da abin da suka yi don sanya mini farin ciki ba,” inji shi.
Yayin da masu karanta labarai mata suka suka soki lamirin manufar wadannan matan, suka kuma nuna tababar cikar hankalin su, wasu kuwa sai “godiya” suke yii musu, musamman saboda suna son zama danshin irin wadannan mata, wajen cusa wa mazajen su farin ciki.