Sun bayar da ni
Wani mahaukaci ne yana tafiya sai ya ga wasu mutane suna Sallar gawa, sai ya shiga sahu shi ma. Da ya ji liman ya yikabbara sai ya ji kowa ya yi kabbara. Da liman ya sake yin kabbara sai mahaukacin nan ya yi ruku’u. Ya duba sai ya ga kowa a tsaye, shi kadai ke […]
Wani mahaukaci ne yana tafiya sai ya ga wasu mutane suna Sallar gawa, sai ya shiga sahu shi ma. Da ya ji liman ya yikabbara sai ya ji kowa ya yi kabbara. Da liman ya sake yin kabbara sai mahaukacin nan ya yi ruku’u. Ya duba sai ya ga kowa a tsaye, shi kadai ke a duke, sai ya dago ya ce: “Ho ’yan nema, sun bayar da ni!”
Daga danladi China Kano 08034463170