Sun bukaci APC ta kame Adamawa kamar yadda ta kame Osun
kungiyar Masu Kishin Jam’iyyar APC, (Forum for Patriotic Members of APC), a karkashin jagorancin Sakatarenta na kasa, Malam Musa Ogah Wukaso ta shawarci uwar jam’iyyar ta kara kwazo wajen ganin ta maimaita nasarar da ta samu a Jihar Osun a zaben Adamawa da za a gudanar a wannan wata. Sakataren ya bayyana haka ne lokacin […]
kungiyar Masu Kishin Jam’iyyar APC, (Forum for Patriotic Members of APC), a karkashin jagorancin Sakatarenta na kasa, Malam Musa Ogah Wukaso ta shawarci uwar jam’iyyar ta kara kwazo wajen ganin ta maimaita nasarar da ta samu a Jihar Osun a zaben Adamawa da za a gudanar a wannan wata.
Sakataren ya bayyana haka ne lokacin da ya ziyarci ofishinmu, inda ya ce manufofin kungiyarsa da kwazonta shi ne ganin jam’iyyarsu ta lashe daukacin zabubbukan badi.
Ya ce, taron kungiyar na kasa ya tabbatar da nada Alhaji Lawal Garba Daura a matsayin sabon shugaban kungiyar na kasa.
“An nada Alhaji Lawal Garba Daura ne, bayan da tsohon shugaban kungiyar, Alhaji Lawal Abubakar baure ya sauka daga mukamin a kashin kansa,” inji shi.
Malam Musa Wukaso ya nanata bukatarsu ta neman goyon bayan al’ummar Najeriya, don kawo sauyi mai ma’ana a fadin kasar nan. Kuma ya bukaci gwamnati ta kula da kiyaye rayuka da dukiyar al’ummar Najeriya, kamar yadda tsarin mulki ya tanada.
kungiyar ta nuna damuwa kan halin da kasa ke ciki, musamman matsalar tsaro da ake fuskanta a yankin Arewa maso Gabas.
Sakataren kungiyar wanda ya jagoranci tawagar ya samu rakiyar Alhaji Abdullahi Abubakar, Shugaban Matasan kungiyar na kasa da kuma Malam Haruna Jibrin, wani jigo a kungiyar.