Sun bukaci sabon Gwamnan Filato ya gyara hanyoyin Jos

Direbobin babur mai kafa uku da aka fi sani da Keke NAPEP a karamar Hukumar Jos ta Arewa da ke Jihar Filato sun bukaci sabon Gwamnan Jihar Barista Simom Lalong ya taimaka ya gyara hanyoyin garin Jos, musamman na karamar hukumar. Shugaban kungiyar direbobin Keke-NAPEP ta kasa (TRUN) reshen karamar hukumar Malam dahiru Hassan ne […]

Sun bukaci sabon Gwamnan Filato ya gyara hanyoyin Jos
Sun bukaci sabon Gwamnan Filato ya gyara hanyoyin Jos

Direbobin babur mai kafa uku da aka fi sani da Keke NAPEP a karamar Hukumar Jos ta Arewa da ke Jihar Filato sun bukaci sabon Gwamnan Jihar Barista Simom Lalong ya taimaka ya gyara hanyoyin garin Jos, musamman na karamar hukumar.

Shugaban kungiyar direbobin Keke-NAPEP ta kasa (TRUN) reshen karamar hukumar Malam dahiru Hassan ne ya yi kiran a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Jos, inda ya ce kungiyarmu ta taka rawa wajen zaben sabon Gwamnan tare da fatar tafiya tare da shi, tare da rokonsa ya gyara hanyoyin cikin garin Jos.
“Wannan ita ce babbar matsalarmu, saboda yawaicin hanyoyin cikin garin Jos sun lalace don haka muna matukar shan wahala saboda lalacewar hanyoyin,” inji shi.
Ya ce zuwa yanzu gwamnatin jihar ta yi rajistar masu Keke-Napep sama da dubu tara, kuma kowanensu ya biya kusan Naira dubu biyar, kafin yin rajistar, baya ga kudin shigar da suke biya a kullum. Don haka ya yi kira ga sabuwar gwamnatin ta dubi gudunmawar da suke bayarwa ta tafi tare da su.
Daga nan ya yi kira ga ’ya’yan kungiyar su ba sabuwar gwamnatin goyon baya da hadin kai, domin ta cimma kudurorin da take dauke da su.