Sun bukaci sarakunan Jihar Zamfara su gyara tsakaninsu da Ministan Tsaro

Wadansu ’yan asalin Jihar Zamfara da ke zaune a Kurmi sun nuna rashin jin dadinsu kan yadda wadansu sarakunan Jihar  Zamfara a matsayinsu na iyaye masu tsawatarwa suka fito suna yin kalaman da za su iya hana ruwa gudu kan matakin yaki da ta’addanci da garkuwa da mutane da mahukunta suka dauka a jihar. Mutanen […]

Sun bukaci sarakunan Jihar Zamfara su gyara tsakaninsu da Ministan Tsaro

Wadansu ’yan asalin Jihar Zamfara da ke zaune a Kurmi sun nuna rashin jin dadinsu kan yadda wadansu sarakunan Jihar  Zamfara a matsayinsu na iyaye masu tsawatarwa suka fito suna yin kalaman da za su iya hana ruwa gudu kan matakin yaki da ta’addanci da garkuwa da mutane da mahukunta suka dauka a jihar.

Mutanen da Aminiya ta zanta da su a garuruwan Legas da Ibadan kan wannan lamari sun nemi a sakaye sunayensu saboda tsoron yiwuwar cin zarafinsu idan sun koma gida.

Mutum na farko ya ce, “Matakin da masu garkuwa da mutane suka fara dauka a Jihar Zamfara ya yi daidai da irin wanda ’yan Boko Haram suka dauka a Jihar Borno a farkon fitowarsu, inda suke sajewa da jama’a suna gudanar da ta’addancinsu. Mutanen gari sun san gidaje da iyayen ’yan Boko Haram amma barazanar hallaka su ta sa suka yi gum da bakinsu a wancan lokaci wanda hakan ya haifar da kazancewar al’amarin zuwa halin da ake ciki yanzu. Irin haka ke faruwa yanzu a Jihar Zamfara inda jama’ar garuruwa da shugabanninsu suke zaune tare da ’yan ta’addan sun san gidaje da iyayensu amma sun kasa tona asirinsu saboda tsoro.”

Mutum na biyu cewa ya yi, “Martanin da sarakunan Jihar Zamfara suka yi wa Ministan Tsaro ba ta dace ba ko kadan domin barazana ce ga tsaro a Jihar Zamfara da kasa baki daya. Ina tunatar da sarakunan a matsayinsu na iyaye ya kamata su san cewa bayanin da Ministan Tsaro ya yi cewa an gano wasu sarakuna a jihar da suke hada baki da masu satar mutane ba shi ne na farko ba. Kafin Ministan ya yi bayanin sai da aka fara samun wadansu sarakuna da suka guje wa garuruwansu a dalilin wannan zargi. Saboda haka ina ganin bai kamata wadannan kalamai su rika fitowa daga bakin sarakunan ba. Kamata ya yi su bar kaza cikin gashinta kada allura ta tono garma.”

Shi ma wani mutumin da wakilinmu ya zanta da shi, ya yi magana ne a kan dakatar da ayyukan hakar ma’adinai a Jihar Zamfara da Gwamnatin Tarayya ta yi, inda ya yi tambayar cewa, “Me ya hana ’yan bindigar kai hari da sace mutane a wuraren hakar ma’adinan? Tunda kudi suke nema to akwai kudin a wannan wuri na hakar ma’adinai a Jihar Zamfara, me ya sa suka ki zuwa can sai a kan talakawa suke cin karensu ba babbaka. Ya kamata a yi binciken kwakwaf a kan wannan al’amari. Gwamnati ta yi daidai da ta dakatar. Duk wanda ya kyamaci matakin gwamnati a kan wannan doka to ya kamata jama’ar Jihar Zamfara su bijire wa al’amarinsa.”