Sun canza gida sau 18 a shekara uku saboda tsoron kyankyaso
An samu wasu ma’aurata da suka rika sauya gidajen zamansu har sau 18 a cikin shekara uku saboda matukar tsoron kyankyaso da uwargidan ke ji. Babu shakka wasu kalilan ne ke son ganin gilmawar kyankyaso, musamman wadanda suke gararamba a cikin dakunan dafa abincinsu. Mun kwato shanu 300 daga hannun barayi a dare daya – […]
An samu wasu ma’aurata da suka rika sauya gidajen zamansu har sau 18 a cikin shekara uku saboda matukar tsoron kyankyaso da uwargidan ke ji.
Babu shakka wasu kalilan ne ke son ganin gilmawar kyankyaso, musamman wadanda suke gararamba a cikin dakunan dafa abincinsu.
- Mun kwato shanu 300 daga hannun barayi a dare daya – Gwamnan Zamfara
- Bidiyon Dala: Na koma Burtaniya har sai kura ta lafa – Jaafar Jaafar
Wata kafar yada labarai ta wallafa wani rahoto, inda kyankyasai suka hana wasu iyalai sakat a garin Bhopal da ke Jihar Madhya Pradesh a kasar Indiya.
Wannan lamari ya faru ne da ma’auratan cikin shekara uku da suka gabata, da nufin samun gidan da baida kyankyasai a ciki.
Ma’auratan dai sun sauya gidaje akalla sau 18 a cikin shekara 3, saboda tsananin tsoron da uwargidan ke ji na kyankyasai da hakan ya sa suke ta hijirar sauya gidaje.
A yanzu da mijin matar ya fara gajiya da yanayin matarsa kuma yana yunkurin tattara bayanan da za su sa a raba aurensu.
Shi dai maigidan yana aiki ne fannin da ya shafi tsarawa da ginawa da gwadawa da kuma kula da manhaja, kuma yana da masaniya kan tsananin tsoron da matarsa ke yi wa kyankyasai wanda wani dan matar yake mata lakabi da suna katsaridaphobia wanda suka haifa bayan aurensu a shekarar 2017.
Wata rana ta dauki numfashi cikin fargaba ta fice daga cikin dakin dafa abinci a guje, wanda hakan ya tsorata duk mutanen cikin gidan kawai sai tayi masu ikirarin cewa, ta ga kyankyaso kuma ba zata sake komawa cikin dakin dafa abincin ba.
Wannan dalili kuma ya sanya ta yi ikirarin cewa mijin nata da su sauya wani sabon gida.
Ma’autan sun fara sauya gidansu na farko ne a shekarar 2018, kuma ba a dade ba matar ta fara nuna matukar tsoro ga kyankyasai, sai suka canza wani gidan.
An ruwaito tun daga wannan lokacin sun sauya gidaje har sau 18, kuma mijin matar ne ke ci gaba da ciyar da gidan duk da kudaden da yake kashewa wajen sauya gidajen.
Ya dauki matar zuwa likitocin kwakwalwa sannan ya ziyarci cibiyar lafiyar tare da matar ta All India Institute of Medical Science (AIIMS), amma ana zargin matar taki amincewa da amfani da magungunan da aka umarceta da tayi amfani da su.
Matar tana matukar tsoron kyankyasai wanda hakan ya sa suka yi ta sauya gidajen zama, sakamakon hakan auren nata samun tangarda da zai iya sanadiyar rabuwarta da mijinta.
A wani bangaren kuma, matar dai ta yi ikirarin cewa, mijin nata bai fahimci matsalarta ba, yana kokarin ya ce tana da matsalar kwakwalwa ne, a bangaren mijin kuma ya ce ya gaji da sauya gidaje don haka yake shirin kashe auren.
A cewar shafin yanar gizo mai wallafa halittun da suke da tsoratarwa na FearOf.net, matar wacce take matukar tsoron kyankyasai kuma ba ta samun kwanciyar hankali idan ta ci karo da kwari.