Sun cire wa matashi hakora a kan budurwa
Kotun Lardi ta Shari’ar Musulunci da ke Gyadi-Gyadi, a birnin Kano ta tsare wadansu matasa biyu bisa zarginsu da lakada wa wani matashi dukan kawo wuka a kan budurwa, inda suka yi sanadiyyar cire masa hakora. dan sanda mai gabatar da kara, Sufeto Yusuf Bello ya shaida wa kotun cewa a makon jiya ne matasan […]
Kotun Lardi ta Shari’ar Musulunci da ke Gyadi-Gyadi, a birnin Kano ta tsare wadansu matasa biyu bisa zarginsu da lakada wa wani matashi dukan kawo wuka a kan budurwa, inda suka yi sanadiyyar cire masa hakora.
dan sanda mai gabatar da kara, Sufeto Yusuf Bello ya shaida wa kotun cewa a makon jiya ne matasan da suka hada da Usman A. Usman da Yusuf Abubakar suka hadu suka yi wa wani matashi mai suna Yusuf Isiyaku duka inda har suka cire masa hakora.
Da yake yi wa kotu karin haske, wanda yake karar ya bayyana cewa matasan sun kasance suna zuwa zance wurin wata budurwa da ke makwabtaka da gidansu, inda shi kuma ya nemi ya hana su saboda ya fahimci suna zuwa ne don su lalata yarinyar. “Kasancewar na fahimci suna zuwa wurin yarinyar ne don su lalata mata rayuwa, sai na yi amfani da damata ta yaya a wurinta, na nemi in hana su zuwa zancen. To hakan ne ya sa suka hadu suka yi mini duka har suka cire mini hakora”, inji shi.
Wadanda ake zargin sun amsa laifinsu, laifin da mai gabatar da kara ya ce ya saba wa sashi na 120 da na 159 na Final Kod.
Alkalin kotun, Mai shari’a Kabir Imam ya dage shari’ar zuwa ranar 31 ga watan da muke ciki tare da bayar da umarnin a tsare wadanda ake zargi a kurkuku.
A wani labarin, an gurfanar da wani mutum mai suna Sadiku Muttaka Gezawa a gaban kotun bisa zarginsa da lakada wa wani tsoho dukan kawo wuka.
dan sanda mai gabatar da kara ya shaida wa kotun cewa dattijon mai suna Alhaji Muhammad Inuwa mai kimanin shekara 90, ya yi kara gaban ’yan sanda cewa bayan wata hatsaniya ta shiga tsakaninsa da Sadiku Muttaka a kan rumfar kasuwa, sai matashin ya dauki wani katon itace ya kwada masa a ka, inda take ya fadi sumamme, lamarin da likitoci suka bayyana cewa ya yi sanadiyar daskarewar jini a kwakwalwarsa.
Dokta Isma’ila Hassan na Asbitin Murtala ya bayyana wa kotun cewa shi ne likitan da ya duba dattijon tare da yi masa aiki a kwakwalwarsa. “Lokacin da aka kai mana dattijon, mun gano cewa sakamakon dukan da aka yi masa, jini ya daskare masa a gefen kwakwalwarsa. A karshe dai mun yi masa aiki a kan hakan,” inji shi.
Sai dai wanda ake zargi ya musanta laifin, wanda mai gabatar da kara ya ce laifi ne da ya saba da sashi na 159 na Final Kod.
An dai dage sauraren shari’ar zuwa ranar 29 ga watan da muke ciki tare da ba da belin wanda ake zargi.