Sun dinke bakunansu don an hana su mafaka

A ranar Litinin da ta gabata ne wasu ’yan gudun hijira daga kasar Iran suka dinke bakunansu da zare da allura a wani mataki na shiga yajin cin abinci saboda an hana su karasawa kasar Macedoniya daga kan iyakar kasar Girka. Iraniyawan wadanda suka yi hijira daga kasarsu zuwa nahiyar Turai, galibinsu kurdawa ne marasa […]

Sun dinke bakunansu don an hana su mafaka
Sun dinke bakunansu don an hana su mafaka

A ranar Litinin da ta gabata ne wasu ’yan gudun hijira daga kasar Iran suka dinke bakunansu da zare da allura a wani mataki na shiga yajin cin abinci saboda an hana su karasawa kasar Macedoniya daga kan iyakar kasar Girka.
Iraniyawan wadanda suka yi hijira daga kasarsu zuwa nahiyar Turai, galibinsu kurdawa ne marasa rinjaye, sun kwashe kimanin kwana hudu suna zanga-zanga a kusa da wani kauye, inda aka kara tsarara sabbin dokiki kan ’yan gudun hijira bayan harin birnin Paris. ’Yan gudun hijirar da sabbin dokokin ba ta shafa ba su ne wadanda suka fito daga kasashen Siriya da Iraki da kuma Afghanistan.
Dubban ’yan gudun hijira daga kasashen Iran da Maroko da kuma Pakistan suna cikin wadanda sabuwar dokar ta fi shafa, inda suka yi arangama da ’yan sanda yayin da suke yunkurin toshe hanyar zirga-zirga tsakanin kasar Girka da Macedoniya.
An ruwaito cewa akalla Iraniyawa shida ne suka dinke bakunansu don nuna rashin gamsuwarsu da sabuwar dokar takaita kwararar ’yan gudun hijirar.
daya daga cikin mutanen wato wani injiniya mai suna Hamid, mai kimanin shekara 34, ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa “ina so na je kowace kasa wadda take kare ’yancin dan Adam, amma ba zan koma wurin da na fito ba saboda za a rataye ni.”