Sun gurfana gaban kotu bisa yi wa amarya kaciya

Rundunar ’yan sanda a Jihar Knao ta gurfanar da wani wanzami da angon wata amarya da kakarsa a gaban kotun Shari’ar Musulunci da ke Gwagwarwa cikin Jihar Kano, bisa zargin su da yi wa amaryar kaciya.dan sanda mai gabatar da kara, Umar Ahmed ya shaida wa kotu cewa mahaifin amaryar ne mai suna Musa Usman […]

Sun gurfana gaban kotu bisa yi wa amarya kaciya
Sun gurfana gaban kotu bisa yi wa amarya kaciya

Rundunar ’yan sanda a Jihar Knao ta gurfanar da wani wanzami da angon wata amarya da kakarsa a gaban kotun Shari’ar Musulunci da ke Gwagwarwa cikin Jihar Kano, bisa zargin su da yi wa amaryar kaciya.
dan sanda mai gabatar da kara, Umar Ahmed ya shaida wa kotu cewa mahaifin amaryar ne mai suna Musa Usman ya kai kara ofishin ’yan sanda, inda ya bayyana cewa surukansa wato kaka da mijin ’yarsa sun dauki ’yarsa mai suna Rukayya Musa Usman wacce shekarunta na haihuwa ba su wuce 15 ba suka sanya wani wanzami mai suna Muhammad Haruna ya yi mata kaciya ba tare da izininsa ba.
Angon amaryar mai suna Sani Muhamamd ya bayyana cewa ba shi ne ya kira wanzami don yi wa amaryar tasa kaciya ba, kakarsa ce ta bayar da wananan umarnin wanda ba zai iya ketarewa ba. “Kakata ce ta shaida min cewa amaryar tawa ba ta da lafiya a gabanta, inda ta kara da cewa ba zan iya kusantarta ba har sai an yi mata aikin angurya. Ita ce ma ta kira wanzamin da ya yi aikin,” inji ango Sani.
Da take bayyana wa kotu yadda lamarin ya faru, kakar angon, Hajiya Amina Yankaba ta bayyana cewa mahaifiyar amaryar ce ta bayar da izinin yi wa ’yarta kaciyar, kasancewar ta fahimci cewa ’yarta tata ba ta da lafiya a gabanta. “Mahaifiyar yarinyar ce da kanta ta zo ta same ni, ta gaya min cewa an yi tsawon wata guda da auren danta da jikana amma har yanzu sha’anin auratayya bai shiga tsakaninsu ba. Ta nuna min cewa in dai har jikan nawa da namiji ne to ya kamata a yau din nan ya yi kwanan aure da ’yarta tata. Hakan ya sa ni kuma da jikan nawa ya dawo na sanar da shi halin da ake ciki, inda kuma na umarce su da su shiga daki su yi kwanan aure. Da na ga an dauki tsawon lokaci da shiga dakinsu ban ji motsinsu ba, sai na kira uwargidan jikan nawa don ta duba min tunda ita mijinsu daya. Da ta je sai ta same su a tsugungune.
“Da ta gaya min halin da ta same su, ni kuma sai na sanar da mahaifiyarta abin da ya faru. Hakan ya sa muka fahimci cewa akwai matsala a tare da amaryar don haka sai muka yanke shawarar gayyato wanzami don ya zo ya duba ta. Da wanzami ya zo sai ya nemi a kaita bayan gida don ya yi mata aiki, inda ya umarci maigidanta da wani mutum su rike ta shi kuma ya cire mata angurya. Ni ba na wurin da aka yi aikin amma dai da zai tafi sai ya dauko wasu abubuwa guda biyu a leda ya ba ni,” inji kakar ango.
Sai dai mahaifiyar amaryar ta musanta cewa ba hannunta a batun yi wa ’yar tata kaciya, hasali ma kakar angon ba ta sanar da ita za ta dauki wannan mataki ba.
A nasa bangaren wanzami Haruna Muhammad wanda ya bayyana wa kotu cewa kakar angon ce ta gayyato shi don ya aiwatar da aikinsa na wanzanci.
“Da ta gayyato ni na zo na duba yarinyar sai na gano tana da matsala. Hakan ya sa na gudanar da aikina a kanta. Tun iyaye da kakanni kowa ya san muna gudanar da wannan aiki a kan matan da suke da matsala a gabansu ba wani sabon abu ba ne. Aikin da na yi yana kan ka’idar aikinmu na wanzanci. Sai dai ina neman afuwar hukuma.”
Dukkanin wadanda ake zargin sun amsa laifinsu, wanda mai gabatar da kara ya ce ya saba da sashe na 121 da 163 da 167 na kundin shari’ar Finalkod na shekarar 2000.
Alkalin Kotun Mohammed Bashir ya dage shari’ar zuwa ranar 3 ga watan gobe tare da bayar da umarnin tsare wadanda ake zargi a kurkuku. Sai dai an bayar da belin kakar ango, Hajiya Amina sakamakon rashin lafiya da tsufa da take fama da shi.